Tsohon Shugaban PDP Kuma Sanata Ya Jefar da Jam’iyyar, Ya Yi Mata Bazata

Tsohon Shugaban PDP Kuma Sanata Ya Jefar da Jam’iyyar, Ya Yi Mata Bazata

  • Tsohon shugaban PDP a jihar Abia, Sanata Emma Nwaka ya watsar da jam'iyyar bayan shafe shekaru da dama
  • Nwaka wanda ya kasance daga ciki wadanda suka assasa jam'iyyar a jihar ya rike shugabancinta na shekaru biyar
  • Jigon PDP ya ce ya yi murabus din ne bayan tunani mai zurfi inda ya ce ya bar dalilan barin jam'iyyar ga karan kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Tsohon sanata kuma jigon PDP a jihar Abia, Emma Nwaka ya yi murabus daga jam'iyyar.

Nwaka wanda yana daga cikin wadanda suka assasa jam'iyyar PDP tun farkon kafa ta ya ce ya barwa kansa dalilin yin haka.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya karbi daruruwan 'yan APC kwanaki kadan da Barau ya yi masa illa

Tsohon sanatan PDP ya yi murabus daga jam'iyyar
Tsohon shugaban PDP, Sanata Emma Nwaka ya watsar da jam'iyyar a Abia. Hoto: Jacob Igwe.
Asali: Facebook

Jigon PDP ya yi murabus daga jam'iyyar

Jigon PDP ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ta godewa Nwaka kan irin gudunmawar da ya ba PDP tun farkon kafa ta zuwa yanzu, ThisDay ta tattaro.

Nwaka ya ce ya dauki matakin ne saboda wasu dalilai na karan kansa wanda sai da ya yi tunani mai zurfi a kai.

Nasarar jam'iyyar PDP karkashin Sanata Nwaka

"Ina matukar godiya da irin damar da aka bani wanda na jagoranci jam'iyyar a jihar Abia na tsawon shekaru biyar."
"Karkashin ikona PDP ta yi nasara a zaben gwamnan har sau biyu a jere da kuma rike ikon Majalisar jihar da nasara a kusan duka zaben Majalisar Tarayya."
"Na yi murabus daga jam'iyyar tun da jimawa kuma bana halartar tarukansu bayan yawan gayyata na da suke yi."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kalu ya bayyana mutum 1 da zai iya kwace mulki daga hannun Tinubu

- Emma Nwaka

Zaben Edo: Dan takarar PDP ya sha alwashi

Kun ji cewa Dan takarar gwamnan jihar Edo a PDP, Asue Ighodalo ya ce ba zai taba bari a juya shi ba idan ya ci zaben gwamnan jihar.

Ighodalo ya bugi kirji inda ya ce zai tabbatar ya kasance mai yanke hukunci ko daukar matakai a karan kansa ba tare da katsalandan ba.

Ighodalo ya ce zai yi kokarin kaucewa duk wasu masu neman juya akalarsa tare da yin taka tsan-tsan wurin gudanar da mulkinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.