Ganduje Ya Tafka Asara, Daruruwan ’Yan APC Sun Watsar da Ita Ana Daf da Zabe
- Yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo a watan Nuwamba, jam'iyyar APC ta tafka asara
- Daruruwan magoya bayan APC sun sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP domin nuna goyon baya ga dan takararsu
- Darakta-Janar na kamfen zaben jam'iyyar, Femi Ikoyi shi ya karbi sababbin tuban a birnin Akure na jihar Ondo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Magoya bayan jam'iyyar APC da dama ne suka watsar da kashinta a jihar Ondo.
Daruruwan mambobin APC sun sauya sheka ne zuwa jam'iyyar SDP ana daf da gudanar da zaben gwamnan jihar.
Ondo: 'Yan jam'iyyar APC sun koma SDP
The Guardian ta ruwaito cewa mambobin sun yi mubaya'a ga dan takarar jam'iyyar, Bamidele Akingboye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mambobin da ke karkashin kungiyar People's Democratic Movement (PDM) sun soki tsarin gudanar da jam'iyyar APC.
Darakta-Janar na kamfen jam'iyyar, Femi Ikoyi ya karbi sababbin tuban a birnin Akure a jiya Talata 27 ga watan Agustan 2024.
Ikoyi ya yi musu alkawarin daidaito tsakaninsu da dukan 'yan jam'iyyar a kowane bangare ba tare da nuna wariya ba, Daily Post ta tattaro.
Ya ce sauya shekar mambobin APC zai kara musu kaimi da kuma ba dan takararsu damar nasara a zaben da za a gudanar.
SDP ta ba tsofaffin 'yan APC tabbaci
"Mun yi murna da samun karuwa, mun taru a nan ne domin nuna goyon baya ga dan takarar SDP, Bamidele Akingboye a zaben watan Nuwambar 2024."
"Wannar kungiya ta yi makamancin haka a zabe lokacin tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko da kuma marigayi, Rotimi Akeredolu."
- Femi Ikoyi
Tallafi: An cafke shugaban APC a Imo
Kun ji cewa wani basarake a Imo ya tabbatar da cafke shugaban APC a gunduma kan zargin karkatar da kayan tallafin Bola Tinubu.
Sarkin Ejemekwuru a karamar hukumar Oguta da ke jihar Imo, Eze Hypolite Obinna Duru shi ya tabbatar da kama Dominic Ikpeama.
Hakan ya biyo bayan ba da tallafi da Mai girma Bola Tinubu ya yi ga jihohin Najeriya 36 saboda halin kunci da 'yan kasar ke ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng