Shiri Ya Baci Ga Ganduje Bayan Babban Jigo a APC Ya Fice Daga Jam'iyyar
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu giɓi bayan ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta ya sanar da ficewa daga cikinta
- Tsohon mai binciken kuɗi APC na ƙasa na APC, Cif George Moghalu, ya aika da wasiƙar yin murabus daga jam'iyyar ga shugabanninta
- Cif Moghalu a cikin wasiƙar ya yiwa jam'iyyar fatan alkhairi inda ya ƙara da cewa ya fice ne saboda wasu dalilai na shi na ƙashin kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Tsohon mai binciken kuɗi na jam’iyyar APC na ƙasa, Cif George Moghalu, ya yi murabus daga jam’iyyar a hukumance.
Tsohon shugaban na hukumar NIWA ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ne a cikin wata wasiƙa da ya aikawa shugabanninta.
Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa Cif George Moghalu ya aika da wasiƙar ne ga shugaban APC na mazaɓar Uruagu 1 da ke Nnewi a ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa jigon APC ya fice daga jam'iyyar?
A cikin wasiƙar yin murabus ɗin na sa daga APC, George Moghalu ya ce ya ɗauki matakin ne saboda dalilai na ƙashin kansa, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Wasiƙar mai dauke da kwanan watan ranar 26 ga watan Agusta, 2024, an kuma miƙa kwafinta ga shugabannin APC a matakin ƙaramar hukumar da jiha.
"Ina son mai sanar da ku cewa na yanke shawarar yin murabus daga zama mamban jam'iyyar APC, daga ranar 26 ga watan Agustan 2024."
"Ina so ku karɓi hakan a matsayin hukunci na ƙashin kaina. Ina matuƙar fatan cewa za mu ci gaba da mutunta alaƙar da ke tsakaninmu wacce muka gina tsawon shekaru."
"Ina yi muku fatan alkhairi tare da sauran mambobin jam'iyyar."
- Cif George Moghalu
Karanta wasu labaran kan APC
- Gwamnan Arewa ya dauki zafi bayan 'yan APC sun yi watsi da Ganduje
- Zaben kananan hukumomi: APC ta ba dan acaba tikitin tsayawa takara a Arewa
- 2027: PDP ta kada hantar Tinubu da APC, ta fadi shirinta na dawowa mulki
Ganduje ya rushe shugabannin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar APC a jihar Benue ya ɗauki sabon salo bayan Abdullahi Umar Ganduje ya kori shugabannin jam'iyyar.
Kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam'iyyar (NWC) ya sanar da rushe shugabannin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Augustine Agada a ranar Laraba, 21 ga watan Agustan 2024.
Asali: Legit.ng