Gwamnatin Tinubu Ta yi Martani bayan an Fara Maganar Haɗarin Zaben APC a 2027

Gwamnatin Tinubu Ta yi Martani bayan an Fara Maganar Haɗarin Zaben APC a 2027

  • Gwamnatin tarayya ta yi martani ga tsohon shugaba a jam'iyyar APC kan kalaman da ya yi a kan kamun ludayin shugaba Bola Tinubu
  • Jami'in shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ne ya yi martanin inda ya ce a yanzu haka sun mayar da hankali a kan wasu abubuwa ne na musamman
  • Tsohon shugaba a jam'iyyar APC, Salihu Lukman ne ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan zargin rashin tsari da manufa mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi martani ga tsohon jigo a jam'iyyar APC, Salihu Lukman kan kalamai da ya yi a kan Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu vs Buhari: Tsohon jigon APC ya 'fadi' shugaban da ya fi lalata kasa

Lukman Salihu ya ce ya kamata jam'iyyun adawa su hada kai wajen kayar da APC a zabe mai zuwa domin ceto Najeriya.

Shugaba Tinubu
Gwamnati ta yi martani ga Lukman Salihu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa jami'in shugaba Bola Tinubu a harkokin sadarwa, Bayo Onanuga ne ya yi martani a madadin gwamnatin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Salihu Lukman a kan Tinubu

Salihu Lukman ya ce an samu lalacewar harkokin gwamnati a karkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Haka zalika tsohon jigon APC ya ce Bola Tinubu ya gaza a kan Goodluck Jonathan yanzu kuma ya dauko hanyar gazawa kan abin da Muhammadu Buhari ya yi.

A karshe, Lukman ya bukaci jam'iyyun adawa da suke rikici da su nemi mafita domin kada Bola Tinubu ya samu zarcewa a 2027 saboda rashin hadin kansu.

Martanin gwamnati ga Lukman

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a halin yanzu ba ta da lokacin da za ta rika musayar yawu da masu nuna adawa da tafiyar Tinubu.

Kara karanta wannan

Yusuf Bichi ya yi murabus: Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar DSS

Bayo Onanuga ya ce da sannu ayyukan da suke domin kawo canji a Najeriya za su ba dukkan yan kasa amsa kan irin maganganun.

Daily Post ta ruwaito cewa Bayo Onanuga ya ce a yanzu haka sun mayar da hankali ne kan ciyar da Najeriya gaba wajen shugabanci nagari.

Lukman ya fadi kuskuren gwamnati

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon darakta-janar na kungiyar gwamnoni, Salihu Lukman ya yi martani kan illar da Bola Tinubu ke yiwa Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa Lukman ya ce tsare-tsaren tattalin arziki na Tinubu suna kashe tattalin kasar madadin farfado da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng