Rikici Na Neman Ruguza APC a Jihar Arewa, Jam’iyya Ta Kira Taron Gaggawa

Rikici Na Neman Ruguza APC a Jihar Arewa, Jam’iyya Ta Kira Taron Gaggawa

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kira wani taro na musamman da ya kunshi manyan jami'yyar a jihar Benue da ke Arewacin Najeriya
  • Hakan na zuwa ne bayan an shafe sama da shekara ana rikicin jam'iyya tsakanin bangaren gwamna da sakataren gwamnati
  • Mataimakin sakataren tsare tsaren jam'iyyar APC na kasa, Nze Chidi Duru ne ya bayyana taron da za su yi a yau domin dinke barakar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Jam'iyyar APC mai mulki ta shirya taro na musamman a kan rikicin shugabanci da ya shafi jihar Benue.

Mataimakin sakataren tsare tsare na kasa na jam'iyyar, Nze Chidi Duru ya bayyana cewa za su tattauna a lokutan mabanbanta kan matsalar jihar Benue.

Kara karanta wannan

Kama jiragen Najeriya: An bukaci DSS ta yi gaggawar kama tsohon gwamnan APC

Gwamna Alia
APC za ta yi taro kan rikicin Benue. Hoto: Tersoo Kula
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugabancin jam'iyyar na kasa zai zauna da bangaren gwamna Hyacinth Alia da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin APC a jihar Benue

Rikicin jami'yyar APC ya kunno kai a Benue ne inda ya shafe sama da shekara ba tare da samun mafita ba.

Hakan ya saka an samu shugabanni biyu, daya mai goyon bayan gwamna Hyacinth Alia daya kuma mai goyon bayan George Akume.

Bayan haka, shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje ya rusa shugabannin jam'iyyar tare da naɗa shugaban riƙon ƙwarya.

Zama domin dinke rikicin APC

Mataimakin sakataren tsare tsare na jam'iyyar APC na kasa, Nze Chidi Duru ya ce za su zauna a Abuja kan rikicin shugabanci a jihar Benue.

Nze Chidi Duru ya bayyana cewa za su zauna karfe 10:00 na safe da bangaren gwamna Hyacinth Alia da George Akume.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: Basarake ya tabbatar da cafke shugaban APC kan almundahana

Haka zalika ya ce za su zauna da misalin karfe 2:00 na rana da shugaban kwamitin riƙon ƙwarya da shugaban jam'iyyar na kasa ya nada.

Gwamna ya yi watsi da zaben fitar gwani

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya nuna rashin amincewa da zaben fitar da gwani da ɓangaren APC ya yi a jihar.

Gwamna Hyacinth Alia ya ce shi ne jagoran APC a jihar kuma bai san da zaben ba saboda haka ya yi kira ga al'umma kan su yi watsi da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng