Gwamnan Arewa Ya Dauki Zafi bayan 'Yan APC Sun yi Watsi da Ganduje

Gwamnan Arewa Ya Dauki Zafi bayan 'Yan APC Sun yi Watsi da Ganduje

  • Gwamnan jihar Benue ya yi gargadi kan jigon jami'yyar APC a jihar, Philip Agbese wanda ya jagoranci wani zaben fitar da gwani
  • Gwamna Hyacinth Alia ya ce bai da masaniya a kan wani zaben fitar da gwani da aka gudanar a jihar domin zaben kananan hukumomi
  • Haka zalika gwamnan ya bayyana cewa hukuncin da shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi a Benue shi ne daidai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya yi martani bayan bangaren APC a jihar ya sanar da yin zaben fitar gwani.

Bangaren APC da Philip Agbese ke jagoranta ne ya ya shirya zaben duk da cewa shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da shi.

Kara karanta wannan

Zaben kananan hukumomi: APC ta ba dan acaba tikitin tsayawa takara a Arewa

Gwamna Alia
Gwamnan Benue ya yi watsti da zaben fitar da gwanin tsagin APC. Hoto: Tersoo Kula
Asali: Facebook

Jami'in yada labaran gwamna Hyacinth, Tersoo Kula ya wallafa a Facebook cewa gwamnan yana kan hukuncin da Abdullahi Ganduje ya zartar a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alia: 'Ba a yi zaben fitar da gwani ba'

Bayan ɓangaren Philip Agbese ya fitar da sakamakon zaben fitar gwani, gwamna Hyacinth Alia ya ce gwamnati ta yi watsi da zaben.

Gwamna Hyacinth Alia ya ce a matsayinsa na jagoran APC a Benue babu wani zaben fitar da gwani da aka yi a kan doka.

Alia ya ce ba a fara sayar da fom ba

Gwamnan Hyacinth Alia ya tabbatar da cewa kwamitin rikon kwarya da Abdullahi Umar Ganduje ya kafa a jihar har yanzu bai fara aiki ba.

Hyacinth Alia ya kara da cewa kwamitin bai fara sayar da fom din zabe ba balle ma ace ya gudanar da zaben fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Ana cikin badakalar kwangila, Gwamna Abba Gida Gida ya rikice da ayyuka a Kano

Gwamna ya yi gargadi kan Philip Agbese

Gwamnan jihar Benue ya ce Philip Agbese ya saba tayar da rikici wajen ƙirƙiro labarai marasa tushe.

Saboda haka ya ce ba shi da lokacin sauraronsa kuma ya yi kira ga al'umma kan su nisnaci abin da yake fada kan shugabancin APC a jihar.

Zamfara: Rikici ya kunno kai a APC

A wani rahoton, kun ji cewa rikicin cikin gida ya sake kunno kai a cikin APC yayin da Sanata Marafa ya sanar da dawowar wani tsagin jam'iyyar.

Tsohon sanatan na Zamfara ta tsakiya ya ce ya farfado da tsagin jam'iyyar ne saboda ya fahimci an cire shi daga sabgar APC a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng