'Dalilin da Ya Sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba Za Su Iya Kayar da Tinubu a 2027 Ba'

'Dalilin da Ya Sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba Za Su Iya Kayar da Tinubu a 2027 Ba'

  • Salihu Lukman ya bayyana cewa kwaɗayin mulki ba zai bar shugabannin adawa su taɓuka komai ba a zaben shugaban ƙasa mai zuwa
  • Tsohon jigon APC ya ce dukkan manyan jam'iyyun adawa suna fama da rikicin cikin gida da faɗa da juna kan abin da bai taka kara ya karya ba
  • Lukman ya ce Atiku, Kwankwaso da Peter Obi, duk fama suke da rikicin cikin gida, wanda hakan ba ƙaramar illa ba ce a a siyasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban APC na Arewa maso Yamma, Salisu Lukman ya ce da wuya ƴan adawa su iya kayar da shugaban ƙasa Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya fadi abin da zai sanya Atiku ya gaza da ya ci zaben 2023

Lukmnan ya yi wannan iƙirari ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 26 ga watan Agusta, 2024.

Salihu Lukman.
Tsohon mataimakin shugaban APC ya ce ƴan adawa ba za su iya kayar da Tinubu ba Hoto: Salihu Lukman
Asali: Twitter

Ya ce manyan jam'iyyun siyasa suna fama da rigingimun cikin gida, wanda a yanzu ta kai ga suna cin amanar juna, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lukman ya hango makomar ƴan adawa

Salihu Lukman ya kafa misali da manyan jam'iyyu PDP da LP, inda ya ce Atiku Abubakar da Peter Obi sun gaza lalaubo bakin zaren rikicin da ya ci su a 2023.

"Abin da takaici, misali shugabannin PDP ba su ga maciji da Atiku Abubakar a daidai lokacin da Peter Obi ke faɗi tashin neman tsira a rigingimun cikin gida na LP.
"Haka ma Sanata Rabiu Kwankwaso ke fama da jam'iyyar NNPP da ta rasa alƙibla. Sauran jam'iyyun adawa kamar SDP da PRP, sun zauna suna jiran wasu ƴan adawa su zo su neme su."

Kara karanta wannan

PDP ta jingine Atiku, ta faɗi wanda za ta iya marawa baya a zaben shugaban ƙasa na 2027

- Salihu Lukman.

'Shugabannin adawa ba su shirya ba'

Tsohon darakta janar na kungiyar gwamnonin APC ya ce son kai, nuna adawa juna da kuma kwadayi ba zai bar jagororin adawar kasar nan su kai labari ba.

Lukman ya ƙara da cewa babu yarda tsakanin shugabannin adawa a yanzu, wanda hakan ba zai bari su iya kifar da gwamnatin Tinubu a 2027 ba, in ji Tribune Nigeria.

An ɗaga taron ASUU da gwamnati

A wani rahoton kuma an samu tsaiko a taron gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'i ASUU wanda aka shirya gudanarwa ranar Litinin.

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Okodeke ya tabbatar da haka, ana tsammani taron ya koma ranar Laraba mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262