Zaben Kananan Hukumomi: APC Ta Ba Dan Acaba Tikitin Tsayawa Takara a Arewa

Zaben Kananan Hukumomi: APC Ta Ba Dan Acaba Tikitin Tsayawa Takara a Arewa

  • Tsohon kansila a jihar Kwara ya samu tikitin tsayawa takara a zaben kananan hukumomi da za a yi a watan Satumba
  • APC ta gabatar da Abdulazeez Jimoh wanda shi ne shugaban kungiyar yan acaba na tsawon lokaci a jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da jihar ke shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Satumbar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Jam'iyyar APC ta ba shugaban yan acaba tikitin tsayawa takara a zaben kananan hukumomi.

Jam'iyyar a jihar Kwara ta ba Abdulazeez Jimoh damar ce domin a dama da shi a zaben da za a yi a watan Satumbar 2024.

APC ta tsayar da shugaban yan acaba takarar zabe a Kwara
Shugaban yan acaba ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban karamar hukuma. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Twitter

APC ta kaddamar da kamfenta a Kwara

Kara karanta wannan

Kama jiragen Najeriya: An bukaci DSS ta yi gaggawar kama tsohon gwamnan APC

An gudanar da bikin mika tuta ga yan takarar a karamar hukumar Irepodun da ke jihar a karshen mako, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan kamfe na jam'iyyar APC, Farfesa Bashir Ibrahim ya ce Jimoh ya cancanci wannan karramawa duba da kokarin da ya ke yi.

Farfesan ya ce irin Abdulazeez karamar hukumar ke bukata domin kawo mata cigaba a bangarori da dama.

Kwara: Jimoh ya bugi kirji kan takararsa

Da yake magana da yan jaridu, Abdulazeez ya ce halin matsi da ake ciki zai taka muhimmiyar rawa a zaben.

"Matsin tattalin arziki da ake ciki ba zai kawo mani cikas ba saboda yanzu zabe ba maganar jam'iyya ba ce sai dai irin jama'a da mutum ke da shi ko kuma sanuwa da ya yi."

- Abdulazeez Jimoh

Jimoh ya rike mukamin kansila da kuma tsohon mataimakin shugaban karamar hukuma kafin samun mukamin shugaban karamar hukumar.

Kara karanta wannan

An samu ci gaba: Kwaleji a Najeriya ta kirkiri abin hawa mai amfani da lantarki

Bauchi: Matashi ya lashe zaben karamar hukuma

Kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya rantsar da shugabannin kananan hukumomi 20 a Bauchi bayan samun nasara a zaben da aka kammala.

Daga cikin ciyamomin da aka rantsar, akwai Pharm. Ibrahim Abubakar Dembo, wani matashi dan shekara 28 da ya ci zabe a karamar hukumar Toro.

Samun nasarar matashi Ibrahim a zaben kananan hukumomin jihar ya kara karsashi a zukatan matasa masu niyyar shiga harkar siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.