Gwamnan APC a Arewa Na Shirin Komawa PDP? Gwamnati Ta Yi Magana
- Gwamnatin jihar Kogi ta fayyace gaskiya bayan ganin Gwamna Usman Ododo a cikin gwamnonin PDP da ake zargin zai sauya sheka
- Gwamnatin ta ce babu kamshin gaskiya kan jita-jitar da ake yadawa cewa Ododo na shirin barin APC domin komawa jam'iyyar PDP
- Wannan martani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Kingsley Fanwo ya fitar a yau Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Gwamnatin jihar kogi ta yi magana kan cece-kuce da ake yi bayan ganin Gwamna Usman Ododo a taron PDP.
Gwamnatin ta ce har zuwa yanzu Gwamna Ododo dan jam'iyar APC ne kuma babu abin da zai fitar da shi a cikinta.
Gwamnati ta ƙaryata cewa Ododo zai koma PDP
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan yada labarai a jihar, Kingsley Fanwo shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Asabar 24 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.
Fanwo ya ce Ododo ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar PDP inda ya ce kawai rashin kwarewar masu yada labarai ne.
"Mun samu rahoton da ke yada cewa Gwamna Ododo na shirin komawa jam'iyyar PDP daga APC."
"Babu kamshin gaskiya a cikin labarin da ake yadawa, mu ne muke da damar yada labarin gaskiya kuma wanda ya dace."
"Masu yada wannan labari ba su gama fita daga gigitar da suka yi ba bayan rasa nasara a Kotun Koli."
- Kingsley Fanwo
Musabbabin haɗuwar Ododo da gwamnonin PDP
Gwamnatin ta ce musabbabin ganin Gwamna Ododo a cikin gwamnonin PDP ya halarci daurin auren yar Gwamna Agbu Kefas ne na jihar Taraba.
Sanarwar ta ce daga cikin wadanda suka halarci daurin auren akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da sauransu.
Ododo ya yi nasara a Kotun Koli
A wani labarin, kun ji cewa Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar zaben jihar Kogi da aka gudanar a watan Nuwambar 2023.
Kotun da ke zamanta a birnin Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Usman Ododo na jam'iyyar APC tare da korar masu korafi.
Asali: Legit.ng