Tallafin Tinubu: Basarake Ya Tabbatar da Cafke Shugaban APC Kan Almundahana

Tallafin Tinubu: Basarake Ya Tabbatar da Cafke Shugaban APC Kan Almundahana

  • Shugaban jam'iyyar APC a gundumar Ejemekwuru a jihar Imo ya shiga hannu kan zargin karkatar da kayan tallafi
  • Ana zargin Mr. Dominic Ikpeama da siyar da wasu daga cikin kayan tallafin Gwamnatin Tarayya a karamar hukumar Oguta
  • Sarkin yankin, Eze Hypolite Obinna Duru ya tabbatar da kama dan siyasar inda ya ce an kai korafi ofishin yan sanda a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - Jami'an tsaro sun yi nasarar cafke shugaban jam'iyyar APC kan badakalar tallafin abinci.

Sarkin Ejemekwuru a karamar hukumar Oguta da ke jihar Imo, Eze Hypolite Obinna Duru shi ya tabbatar da haka.

Shugaban APC ya shiga hannu kan badakalar kayan tallafin Tinubu
Jami'an tsaro sun kama shugaban APC kan almundahana da kayan tallafin Bola Tinubu. Hoto: Hope Uzodinma.
Asali: Facebook

Tallafin Tinubu: An shugaban APC kan badakala

Kara karanta wannan

Ana zargin wasu Ƴan daba sun farmaki magoya bayan APC a harabar kotun ƙoli

Tribune ta ruwaito cewa an kama shugaban jam'iyyar a gundumar Ejemekwuru, Mr. Dominic Ikpeama kan zargin badakala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Ikpeama da siyar da kayan tallafin da Gwamnatin Tarayya ta bayar da aka ware domin yankin.

Basaraken ya ce an yi nasarar cafke dan siyasar ne bayan korafi a ofishin yan sanda game da siyar da wasu buhunan kayan abincin.

"Wannan abin da Ikpeama ya aikata bai kamata ba kuma wadanda aka kawo kayan dominsu ba su ji dadin haka ba."
"An tsare Ikpeama a ranar Laraba 21 ga watan Agustan 2024 a ofishin yan sanda na yankin Oguta."

- Eze Hypolite Obinna Duru

Shugaban APC ya yi magana kan zargin

Yayin da aka tuntubi Ikpeama kan zargin da ake yi masa, ya yi fatali da hakan inda ya ce ya raba kayan tallafin a manyan kauyuka biyar.

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Dattawan Arewa sun yi martani kan lamarin, sun tura sako ga Sultan

Ya bayyana cewa an sako shi daa kulle inda yan sanda suka ce ya tafi gida domin yin sulhu da yan yankin.

Kano: APC ta bukaci binciken badakalar Novomed

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen Kano ta nemi hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta binciki gwamnatin jihar bisa zargin kwangila.

A sanarwar da shugaban jam'iyya a Kano, Abdullahi Abbas ya fitar, ya ce akwai ayar tambaya kan zargin baya-bayan nan na ba kamfanin Novomed kwangilar miliyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.