Gwamnan APC Ya Aika Sako Ga 'Yan Adawa Bayan Nasara a Kotun Koli
- Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yi magana kan nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli a shari'ar zaɓen gwamnan jihar
- Gwamna Ododo ya yaba da hukuncin na Kotun Ƙoli wanda ya tabbatar da shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamman jihar
- Gwamnan na Kogi ya yi kira ga ƴan adawa da su zo a haɗa ƙarfi da ƙarfe da su domin a ciyar da jihar gaba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo ya yaba da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar sa a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar.
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana nasarar a matsayin hukuncin Allah maɗaukakin Sarki.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ismail lsah ya fitar a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Gwamna Ododo ya ce kan nasararsa?
Gwamnan ya buƙaci ƴan adawa da su zo a haɗa ƙarfi da ƙarfe da su domin ciyar da jihar gaba, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Gwamna Ododo ya kuma buƙaci magoya bayansa da mambobin jam'iyyar APC su gudanar da bukukuwan murnar nasararsa cikin natsuwa da lumana.
"Wannan nasarar ba ta wa ba ce ni kaɗai. Nasara ce ga mutanen da suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu domin zaɓen mu a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023 kuma muka yi nasara."
"Zaɓen ingantacce ne kuma an gudanar da shi bisa gaskiya. A tarihin jihar mu shi ne zaɓe wanda yafi kowane rashin rikici."
"Ina kira ga ƴan uwa na jam'iyyun adawa da su zo su taya ni ciyar da jihar Kogi gaba."
Ahmed Usman Ododo
Matasa sun farmaki ɗan takarar gwamna
A wani labarin kuma, kun ji cewa jim kaɗan bayan yanke hukunci a Kotun Koli, yan daba sun farmaki dan takarar gwamna a jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Matasan sun kai farmaki kan dan takarar na jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka duk da rashin nasara da ya yi a Kotun Koli kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng