Ana Zargin Wasu Ƴan Daba Sun Farmaki Magoya Bayan APC a Harabar Kotun Koli
- Jam'iyyar APC ta yi ikirarin cewa an farmaki magoya bayanta a harabar kotun koli bayan yanke hukunci kan zaben jihar Kogi
- Kakakin kwamitin kamfen APC na jihar Kogi, Kingsley Fanwo ya ce suna zargin magoya bayan Murtala Ajaka ne suka farmake su
- Sai dai jam'iyyar SDP ta ce wannan karya ce da yaudara domin su ya kamata su yi ƙorafi bisa harin da magoya bayan APC suka kai masu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Jam’iyyar APC reshen Kogi ta yi ikirarin cewa an kai wa magoya bayanta hari tare da lalata motocinsu a harabar kotun koli ranar Juma’a.
Daraktan yaɗa labarai na kwamitin kamfen APC na jihar Kogi, Kingsley Fanwo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja.
Ya ce lamarin ya faru ne lokacin da magoya bayan jam’iyyar SDP suka fara jifan magoya bayan APC da duwatsu, kwalabe da robobi, in ji Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Fanwo ya ce hakan ta faru ne jim kaɗan bayan kotun koli ta yanke hukuncin ta tabbatar da Gwamna Usman Ododo a matsayin zababben gwamnan Kogi.
APC ta zargi magoya bayan SDP
Jigon APC ya kuma yi ikirarin cewa dan takarar SDP, Murtala Ajaka, ya yi biris da shawarar da kotu, wadda ta nemi kowa ya zauna a wurin da yake har sai ta gama karanto hukunci.
Kingsley Fanwo ya ce Murtala Ajaka ya tashi ya bar kotun tare da magoya bayansa saboda hukuncin ya masa zafi.
"Da suka lura da ‘yan APC suna murna a harabar kotun, magoya bayan Ajaka suka far masu da neman rigima wanda hakan ya haddasa hayaniya a harabar kotun," in ji shi.
SDP ta maida martani ga APC
Da yake mayar da martani, mai magana da yawun kwamitin kamfen Muri/Sam na SDP a Kogi, Isaiah Ijele, ya bayyana ikirarin APC a matsayin karya da yaudara.
Mista Ijele ya ce dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP, Mista Ajaka, da magoya bayansa ne aka kai wa hari, ba magoya bayan APC ba.
A rahoton Channels tv, Ijele ya ce:
"Mu ya kamata mu yi korafi tare da yin Allah wadai da abin da magoya bayan jam’iyyar APC suka mana ba, ba ku ba."
Gwamna Ododo ya naɗa hadimai 1,192
A wani rahoton kuma Gwamna Ahmed Usman Ododo ya naɗa sababbin hadimai 1,192 waɗanda suka fito daga faɗin kananan hukumomin jihar Kogi.
Sakatariyar gwamnatin Kogi, Dr. Folashade Ayoade ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar, ta ce za su fara aiki ranar 1 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng