"Ka da Ka Bata Mana Suna": Gwamnonin PDP Sun Soki Tinubu kan Tallafi, Sun Ba da Shawara

"Ka da Ka Bata Mana Suna": Gwamnonin PDP Sun Soki Tinubu kan Tallafi, Sun Ba da Shawara

  • Gwamnonin jihohi a karkashin jam'iyyar PDP sun koka kan yadda ake zargin su game da tallafin Gwamnatin Tarayya a kasar
  • Gwamnonin sun bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gargadi mukarrabansa kan neman hada su rigima da al'umma
  • Sun koka kan yadda gwamnatin ta mayar da hankali kan tallafi da ba zai rage komai ba madadin nemo hanyar ragewa jama'a radadi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - Gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun caccaki Bola Tinubu kan tallafi da ya ba jihohi.

Gwamnonin sun koka kan yadda ake yada maganganu kan tallafi wanda ba zai wadatar da jihohin ba.

Gwamnonin PDP sun fusata kan zarginsu game da tallafi
Gwamnonin PDP sun shawarci Bola Tinubu game da rage radadi a Najeriya. Hoto: Sen. Bala Mohammed.
Asali: Facebook

Tallafi: Gwamnonin PDP sun gargadi Tinubu

Kara karanta wannan

Bayan kamfanin China ya kwace kadarori a waje, an kai gwamnatin Tinubu kotu a gida

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a Jalingo na jihar Taraba a jiya Juma'a 23 ga watan Agustan 2024, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin sun bukaci Tinubu ya gargadi mukarrabansa kan neman hada su fada da jama'a.

Suka ce kwata-kwata babu abin da tallafin zai rage duba da halin kunci da ake ciki a kasar na tsadar rayuwa, Channels TV ta tattaro.

"Muna bukatar Tinubu ya ja kunnen mukarrabansa kan neman hada mu rigina da mutane game da tallafi da ba zai rage komai ba."
"Madadin samar da yanayin tattalin arziki mai kyau, Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali wurin cece-kuce da zarge-zarge kan tallafin."

- Cewar sanarwar

Gwamnonin PDP sun himmatu wurin rage radadi

Gwamnonin daga bisani sun bayyana himmatuwarsu wurin tabbatar da rage radadi ga al'ummarsu.

Wannan na zuwa ne bayan tallafi tireloli 20 ga jihohin Najeriya 36 da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin rage radadi.

Kara karanta wannan

Mutumin Jonathan ya tono makircin da ake shiryawa Tinubu a Arewa bayan sayen jirgin sama

Zanga-zanga: Gwamnonin PDP sun shawarci Tinubu

Kun ji cewa Gwamnonin da suka ɗare kan madafun iko a inuwa jam'iyyar PDP sun gudanar da taro a jihar Taraba ranar Jumu'a.

A taron, gwamnonin ƙarƙashin inuwar kungiyar gwamnonin PDP sun tattauna batutuwa da dama ciki har da batun waɗanda aka kama lokacin zanga-zanga.

Gwamnonin PDP sun kuma bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da waɗanda aka kama yayin zanga-zangar a gaban kotu kuma a yi masu adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.