PDP Ta Jingine Atiku, Ta Faɗi Wanda Za Ta Iya Marawa Baya a Zaben Shugaban Ƙasa na 2027
- Jam'iyyar PDP ta ƙasa ta nuna a shirye take ta marawa Goodluck Jonathan baya idan ya amince zai dawo a babban zaɓen 2027
- Mataimakin sakataren yaɗa labaran PDP, Ibrahim Abdullahi ya ce dama ba a yi wa tsohon shugaban ƙasar adalci ba a sukar da aka masa kan tsaro
- Wannan na zuwa a daidai lokacin da aka fara kiraye-kirayen Jonathan ya sake fitowa takara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar jami'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta bayyana cewa a shirye take ta marawa tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan baya a zaɓen 2027.
PDP ta bayyana aniyar miƙawa Jonatahn tikiti idan ya amince zai dawo ya yi takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.
Mataimakin sakataren yaɗa labaran PDP ta ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya shaidawa Daily Trust cewa duk da wahalhalun da ake ciki, ƴan Najeriya ba su manta da Jonathan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP na maraba da dawowar Jonathan
Ibramin ya ayyana tsohon shugaban ƙasan a matsayin jagora wanda Najeriya ke buƙata a halin yanzu.
“A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ta gaza magance matsalolin kasar nan, dawowar Goodluck Jonathan zai zama abin farin ciki. PDP za ta mara masa baya domin ɗanta ne.
"Ƴan Najeriya sun fahimci cewa Jonathan shugaba ne da za su iya dogaro da shi, a shekaru shida na mulkinsa, ya daidaita farashin kayayyaki, canjin Naira da tattalin arziki."
Kakakin PDP ya ƙara da cewa dama ba a yi wa gwamnatin Jonathan adalci ba wajen sukar da aka mata musamman a fannin tsaro, rahoton jaridar Pulse.
Matsaloli sun ƙaru a mulkin Buhari
Ibrahim ya ambaci yadda aka samu ƙarin matsalolin tsaro a mulkin Muhammadu Buhari da APC kamar rikicin manoma da makiyaya da kuma yawaitar ‘yan bindiga.
"Karerayin da aka yaɗa a lokacin Jonathan dangane da tsaro yanzu gaskiya ta yi halinta. Shi kansa tsohon shugaban ƙasa, Janar mai ritaya ya gaza murƙushe Boko Haram da Jonathan ya kusa ganin bayanta a 2015."
Ganduje, Kwankwaso da Atiku sun haɗu
A wani rahoton kuma jiga-jigan siyasar Najeriya da dama sun samu halartar daurin auren ɗiyar Atiku Abubakar a yau Juma'a a birnin Abuja.
Yayin daurin auren an gano Sanata Rabiu Kwankwaso da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje da wasu jiga-jigan siyasar Najeriya a wurin.
Asali: Legit.ng