Kogi: Kotun Koli Ta Yi Hukuncin Karshe kan Takaddamar Zaben Gwamnan APC, Ta Jero Dalilai

Kogi: Kotun Koli Ta Yi Hukuncin Karshe kan Takaddamar Zaben Gwamnan APC, Ta Jero Dalilai

  • Kotun Koli ta yanke hukunci kan rigimar zaben jihar Kogi da aka gudanar a watan Nuwambar shekarar 2023 da ta gabata
  • Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Usman Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar
  • Ta kuma yi fatali da korafe-korafen dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka saboda rashin gamsassun hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar zaben jihar Kogi da aka gudanar.

Kotun da ke zamanta a birnin Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Usman Ododo na jam'iyyar APC.

Kotun Koli ta yi hukunci kan zaben gwamnan Kogi
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Usman Ododo na APC a zaben jihar Kogi. Hoto: Usman Ododo, Murtala Ajaka.
Asali: Twitter

Zaben Kogi: Hukuncin da kotu ta yanke

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, kotun koli ta yanke hukunci kan sahihancin zaɓen gwamnan APC

TheCable ta tattaro cewa kotun ta yi fatali da korafin dan takarar jam'iyyar SDP a zaben, Murtala Ajaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin Alkalan kotun mai dauke da mutane biyar ne ya yanke hukuncin a yau Juma'a 23 ga watan Agustan 2024.

Kotun ta kuma kori korafin dan takarar gwamna a jam'iyyar AA a zaben, Olayinka Baimoh saboda rashin gamsassun hujjoji, cewar The Nation.

Sadiq Umar shi ne ya karanto korafe-korafen guda uku da ake kalubalantar zaben gwamnan Kogi, Usman Ododo a watan Nuwambar 2023.

Kogi: Kotu ta ci tarar masu korafi

Daga bisani kotun ta ci tarar wadanda suke korafin da kudi har N5m bayan ta fatattaki korafe-korafen nasu a shari'ar.

A zaben watan Nuwambar da ka gudanar, Ododo ya samu kuri'u 446,237 yayin da Murtala Ajaka na SDP ya samu 259,052 sai kuma Dino Melaye na PDP ya samu 46,362

Kara karanta wannan

Jigawa: Mutuwar aure ta jawo bazawara ta watsa fetur, ta kona kanta kurmus

Kotun koli ta raba gardama a zaben Bayelsa

Kun ji cewa Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa a zaɓen da aka yi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Kotun ta kori ƙarar da tsohon ƙaramin ministan man fetur, Timipre Sylva ya ɗaukaka zuwa gabanta yana ƙalubalantar nasarar Diri.

Mai shari'a Mohammed Lawal shi ne ya karanto hukuncin kotun a madadin kwamitin alkalai biyar yau Jumu'a, 23 ga watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.