Atiku Abubakar Ya 'Gano' Shirin Shugaba Tinubu da Iyalansa Akan Najeriya

Atiku Abubakar Ya 'Gano' Shirin Shugaba Tinubu da Iyalansa Akan Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da hada baki da iyalansa wajen cutar yan Najeriya
  • Atiku Abubakar, wanda shi ne tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya kara da cewa abokan Tinubu ma na da hannu a batun
  • Atiku ya kara da cewa ko bayan gwamnatin Tinubu ta shude, za a sha wahala kafin gyara kura-kuran da ake tafkawa a gwamnatin nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kokarin lalata kasar nan.

Haka kuma Atiku Abubakar na ganin iyalan shugaba Tinubu da abokansa na kokarin cefanar da kasar nan gabanin kammala wa'adinsa.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gano inda tallafin buhunan shinkafar Tinubu ke maƙalewa

Atiku
Atiku Abubakar ya zargi Tinubu da shirin ruguza Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya yi zargin cewa a halin da ake tafiyar da kasar nan, sai an sha wahala kafin a gyara barnar da tafka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta sanarwar da hadimin Atiku, Paul Ibe ya sanyawa hannu, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce Tinubu na mulkin kasar nan kamar yadda ya yi a Legas.

Atiku ya zargi iyalan Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaici kan niyyar gwamnati na cefanar da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL).

Ya ce akwai zargi mai karfi kan yadda kamfanin Oando ke daukar kwangilar fetur, wanda kuma mallakin dan uwan shugaban kasa, Wale Tinubu.

The Cable ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya kara da zargin gwamnati ta bar Mele Kyari a matsayin shugaban NNPCL saboda yadda ya ke taimakawa a aikata da daidai ba.

Kara karanta wannan

El Rufai ya jagoranci tawaga zuwa gidan Atiku, bayanai sun fito

NNPCL ya wanke iyalan Tinubu

A wani labarin kun ji cewa shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya musanta cewa iyalan shugaban kasa, Bola Tinubu na juya shi yadda su ka ga dama.

Kan zargin kulla alaka da wani yanki na kamfanin man Oando, OVH, da ke mallakin yan uwan shugaba Tinubu NNPCL ya bayyana cewa ya ginu ne kan samar da riba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.