Jigawa: Masu Zanga Zanga Sun Kewaye Gidan Gwamnati, Sun Faɗi Buƙatarsu

Jigawa: Masu Zanga Zanga Sun Kewaye Gidan Gwamnati, Sun Faɗi Buƙatarsu

  • Wasu gungun mutane daga ƙaramar hukumar Ringim sun yi zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar Jigawa da ke Dutse ranar Alhamis
  • Masu zanga-zangar sun bukaci Gwamna Umar Namadi ya tsige kwamishinan noma, Muttaka Namadi wanda ya fito daga yankin Ringim
  • Jagoran masu zanga-zangar, Abdullahi Muhammad ya ce kwamishinan ba ya wakiltarsu yadda ya kamata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Wasu gungun masu zanga-zanga daga karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa sun yi tattaki zuwa gidan gwamnatin jihar da ke Dutse ranar Alhamis.

Masu zanga-zangar sun buƙaci Gwamna Umar Namadi ya sauke kwamishinan noma, Muttaka Namadi, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Ringim.

Gwamna Umar Namadi.
Masu zanga-zanga sun yiwa gidan gwamnatin jihar Jigawa kawanya Hoto: Umar Namadi
Asali: Twitter

Masu zanga-zanga sun mamaye gidan gwamnati

Kara karanta wannan

Ana tsaka da cacar baki kan bidiyon Dan Bello, Abba ya runtumo babban aiki a Kano

A cewarsu, kwamishinan ba ya wakiltar yankin yadda ya kamata a majalisar zartaswa ta jihar Jigawa, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga zangar sun tare babbar kofar shiga gidan gwamnati suna rera kalamai na batanci tare da nuna rashin jin dadinsu da halayen Muttaka Namadi.

Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar, Abdullahi Muhammad, ya ce dukkansu 'ya’yan jam’iyyar APC ne da suka fito daga gundumomi 10 na karamar hukumar Ringim.

Menene dalilin wannan zanga-zanga?

A rahoton Daily Trust, Abdullahi ya ce:

“Mun zo nan ne domin mu gabatar da korafinmu a hukumance kan kwamishinan noma, Muttaka Namadi saboda rashin ingancin wakilcin da yake wa yankin mu.
"Mun masa magana domin ya gyara ya tafi da kowa amma ya yi kunnen uwar shegu da mu. Mun yanke shawarar zuwa nan ne kamar yadda gwamna ya ce duk wanda ya naɗa a mukami ya jawo kowa a jikinsa.

Kara karanta wannan

Farfesa ya hango abin da zai tayar da hankalin Tinubu, ya yi gargadi

"Tun da kwamishinan ya ƙi bin umarnin gwamna ba mu da wani zaɓi face mu nemi a sauke shi daga matsayin mamban majalisar zartaswa, a naɗa wani daga Ringim."

Yadda aka tarbi masu zanga-zangar

Shugaban ma’aikatan gwamna, Mustapha Makama da shugaban APC na jihar, Aminu Sani ne suka tarbi masu zanga-zangar a ƙofar shiga fadar gwamnati.

Sun kuma yi masu alkawarin cewa za su isar da sakonsu ga Gwamna Umar Namadi.

Wani jigon PDP a Kano ya koma APC

A wani rahoton kuma Sanata Barau I Jibrin ya karɓi ɗaya daga cikin kusoshin jam'iyyar PDP a jihar Kano wanda aka fi sani da Alin Kano zuwa APC.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce sauya sheƙar fitaccen ɗan siyasar zai ƙarawa APC karfi a Kano da ƙasa baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262