Ganduje: Ɗaya Daga Cikin Ƙusoshin Siyasa a Kano Ya Sauya Sheka Zuwa APC

Ganduje: Ɗaya Daga Cikin Ƙusoshin Siyasa a Kano Ya Sauya Sheka Zuwa APC

  • Sanata Barau I Jibrin ya karɓi ɗaya daga cikin kusoshin jam'iyyar PDP a jihar Kano wanda aka fi sani da Alin Kano zuwa APC
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce sauya sheƙar fitaccen ɗan siyasar zai ƙarawa APC karfi a Kano da ƙasa baki ɗaya
  • Alhaji Abdullahi Ali, watau Alin Kano ya ce fiye da shekaru 30 da suka wuce yana koyi da kayawawan ɗabi'un Sanata Barau Jibrin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin ya karbi babban jigon kuma ginshiƙi a jam’iyyar PDP ta jihar Kano.

Alhaji Abdullahi Ali wanda aka fi sani da Alin Kano, ɗaya daga cikin ƙusoshin PDP a jihar Kano ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

A karon farko bayan fara rikicin sarauta, Sarki na 15 Aminu Ado ya fita daga Kano

Sanata Barau I Jibrin.
Sanata Barau ya karɓi babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Kano Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Leadership ta ce Alin Kano, wanda ya yi ƙaurin suna a jam'iyyar PDP ta ƙasa, ya fito ne daga ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da ke mazaɓar Sanatan Kano ta Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alin Kano ya ziyarci Barau a Abuja

Sanata Barau ya karɓi wannan babban kamu da APC ta yi a Kano a ofishinsa da ke zauren majalisar tarayya a Abuja ranar Alhamis.

Da yake masa maraba zuwa jam’iyya lamba ɗaya a Afirka watau APC, Sanata Barau ya bayyana Alin Kano a matsayin dan siyasa mai ƙwazo da gaskiya.

Barau ya ƙara da cewa Alin Kano mutum ne wanda a kodayaushe yake kan gaba a harkokin da suka shafi matasa da dalibai a kowane mataki.

Mataimakin shugaban majalisar dattawar ya ce sauya shekar Alin Kano zuwa APC nasara ce kuma zai karawa jam'iyyar ƙarfi a Dawakin Kudu, Kano ta Kudu da ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai sake shillawa ƙasar waje awanni kaɗan bayan ya dawo Najeriya

'Jam'iyyar APC ta ƙara ƙarfi a Kano'

A rahoton Daily Trust, Sanata Barau ya ce:

“A yau, muna farin cikin maraba da wannan matashin dan siyasa mai himma kuma sananne, Alin Baba zuwa jam’iyyarmu, a da shi ƙusa ne a PDP kafin ya shigo cikin APC.
"Hakan ya ƙara mana ƙarfi domin tun ba yau ba mun san shi kuma mun san abin da zai iya. Kamar yadda kuke gani har ya kama aiki, ya zo nan tare da shugabannin APC na Dawakin Kudu."

Da yake tabbatar da shiga APC, Alhaji Abdullahi Alin Kano ya ce Sanata Barau ya kasance mutum na gari wanda yake koyi da shi fiye da shekaru 30.

Gwamna ya nesanta kansa da cin hanci

A wani rahoton na daban gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya ce ba za a zarge shi da cin kuɗin haram ba ko ya bar mulki saboda ba ya wuce halal ɗinsa.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya faɗi gaskiya kan jita jitar yana shirin sauya sheƙa

Uzodinma ya ba ma'aikatan gwamnati da masu rike da muƙaman siyasa shawarin su tsaya a iya halal din da Allah ya ba su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262