APC Na Neman Birkicewa Bayan an Maka Ganduje Kara gaban Kotu
- Korarrun shugabannin APC a.jihar Benue ba su gamsu da sauke su daga kan muƙamansu da NWC tayi ba
- Shugabannin sun maka kwamitin na NWC ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ƙara a gaban kotu
- Sun buƙaci a tilasta mayar da su kan muƙamansu tare da ɗaukar mataki kan Ganduje saboda sabawa kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam'iyyar APC a jihar Benue na ci gaba da ɗaukar zafi.
Korarrun shugabannin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Augustine Agada sun maka shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ƙara a gaban kotu.
APC: Meyasa aka kai Ganduje ƙara?
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa shugabannin sun kai Ganduje ƙara ne saboda yin biris da umarnin kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Laraba, babbar kotun jihar Benue dai ta hana kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam'iyyar APC (NWC) ƙarƙashim jagorancin Ganduje, rushe shugabannin APC na jihar ƙarƙashin jagorancin Augustine Agada.
Sai dai, da yammacin ranar Laraba, Ganduje ya sauke shugabannin duk da umarnin da kotun ta bayar.
An maka Ganduje ƙara a kotu
A ranar Alhamis, Augustine Agada tare da wasu mutum takwas suka shigar da ƙara kan kwamitin na NWC ƙarƙashin jagorancin Ganduje, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
A cikin ƙarar mai lamba MHC/1585/M/2024, Agada da sauran shugabannin sun buƙaci ta tilastawa Ganduje bin umarninta na hana rushe su har sai wa'adinsu na shekara huɗu ya ƙare.
Korarrun shugabannin sun kuma buƙaci kotun da ta ɗauki mataki mai tsauri a kan kwamitin NWC ƙarƙashin jagorancin Ganduje saboda ƙin bin umarnin da ta bayar.
Batun takarar Ganduje a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nesanta kansa da fastocin takarar shugaban ƙasa da ke yawo a soshiyal midiya.
Ganduje ya musanta raɗe-raɗin cewa yana shirin fitowa takarar shugaban ƙasa tare da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma a babban zaɓen 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng