Gwamna Ya Bugi Ƙirji, Ya Ce Ba Wanda Zai Tuhume Shi da Satar Kuɗin Talakawa

Gwamna Ya Bugi Ƙirji, Ya Ce Ba Wanda Zai Tuhume Shi da Satar Kuɗin Talakawa

  • Gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya ce ba za a zarge shi da cin kuɗin haram ba ko ya bar mulki saboda ba ya wuce halal ɗinsa
  • Uzodinma ya ba ma'aikatan gwamnati da masu rike da muƙaman siyasa shawarin su tsaya a iya halal din da Allah ya ba su
  • Gwamnan ya ce rashin gaskiya da burin tara dukiya ta kowane hali ke jawo ƙaruwar cin hanci da rashawa a ƙasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya ce babu wanda zai tuhume shi da yin sama da faɗi da dukiyar al'umma bayan ya sauka daga mulki.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da lakca a taron tunawa da Michael Okpara a cibiyar Musa Yar’Adua da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta dauki barazanar ASUU da gaske, ta na neman hana yajin aiki

Gwamna Hope Uzodinma.
Gwamnan Imo ya bukaci masu rike da muƙaman gwamnati su ji tsoron Allah, su tsaya a kan halak ɗinsu Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Twitter

Gwamna Uzodinma ya ba shugabanni shawara

Uzodinma, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC ya shawarci masu riƙe da muƙaman gwamnati su tsaya iya inda Allah ya aje su, su kaucewa cin haram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Hope Uzodinma ya bukaci ma'aikata da masu rike da muƙaman siyasa su ci iya halal ɗin da Allah ya ba su.

Gwamna Uzodinma ya ce akwai bukatar shugabannin siyasa su yi koyi da halayen marigayi Firimiyan Gabashin Najeriya, Michael Okpara.

A cewarsa, neman tara dukiya ido rufe, da rashin kyawawan ɗabi'u su ne asalin tushen abubuwan da ke kawo cin hanci da rashawa a Najeriya.

Gwamna ya taɓo aikin wutar lantarki

Game da ayyukansa a Imo, Uzodinma ya ce tashar wutar lantarki ta Egbema da yanzu haka ake yi mata ƴan gyare-gyare, za a kammala aiki kuma ta fara aiki a farkon 2025.

Kara karanta wannan

Wike ya yi maganar yiwuwar sasantawa kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Ya ce aikin na da matuƙar muhimmanci domin ana sa ran tashar za ta taka rawa wajen samar da wutar lantarki ta tsawon awanni 24 a faɗin jihar Imo.

Sauran bakin da suka halarci taron sun hada da gwamnan jihar Cross River, Prince Bassey Otu, mataimakiyar gwamnan jihar Ebonyi, Patricia Obila da sauransu.

Alkalin Alkalan Najeriya ya yi ritaya

A wani rahoton kuma Alkalin Alƙalan Najeriya na 22, Olukayode Ariwoola ya yi ritaya daga aiki bayan cika shekaru 70 a duniya.

Mai shari'a Ariwoola ya zama Alkalin Alkalan Najeriya ne a watan Yuni, 2022 bayan magabacinsa, Tanko Muhammad ya yi murabus.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262