Duk da Umarnin Kotu, Jam'iyyar APC Ta Rushe Shugabanninta, Ta Fadi Dalili

Duk da Umarnin Kotu, Jam'iyyar APC Ta Rushe Shugabanninta, Ta Fadi Dalili

  • Kwamitin gudanarwa na ƙasa na APC (NWC) ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ya sauke shugabannin jihar Benue
  • Kwamitin na NWC ya ɗauki matakin ne duk da umarnin da babbar kotun jihar Benue ta ba da wanda ya hana sauke shugabannin
  • A madadin shugabannin da aka sauke, NWC ya ƙaddamar da shugabannin riƙon ƙwarya da za su jagoranci jam'iyyar a jihar Benue

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar APC a jihar Benue ya ɗauki sabon salo.

Kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam'iyyar (NWC) ya sanar da rushe shugabannin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Augustine Agada a ranar Laraba, 21 ga watan Agustan 2024.

APC ta rushe shugabanninta a Benue
APC ta kori shugabanninta na jihar Benue Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

APC ta ƙaddamar da kwamitin riƙon ƙwarya

Kara karanta wannan

Batun tsige Akpabio: Kungiyar tsofaffin tsagerun Neja Delta ta yi gargadi

A madadinsu, kwamitun na NWC ya ƙaddamar da kwamitin riƙon ƙwarya mai mutum bakwai wanda zai jagoranci ragamar jam'iyyar a jihar na tsawon wata shida, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon kwamitin ya ƙunshi Benjamin Omale a matsayin shugaba sai Farfesa Bem Angwe a matsayin sakatare.

Sauran 'yan majalisar sun haɗa da Richard Mzungweve, James Ornguga, Terhemen Ngbea, Helen Agaigbe da Ali Francis Adah.

Jam'iyyar APC ta yi biris da umarnin kotu

Sauyin shugabancin da aka samu na zuwa ne ƴan awanni kaɗan bayan babbar kotun jihar Benue ta hana jam'iyyar APC cire Augustine Agada da sauran shugabannin jam'iyyar.

A hukuncin da mai shari'a Theresa Igoche ta yanke a ƙarar mai lamba MH/1585m/2024, an hana kwamitin NWC ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje cire shugagannin har sai wa'adinsu na shekara huɗu ya cika.

Jam'iyyar APC a jihar Benue dai na takun saƙa da Gwamna Hyacinth Alia kan shugabancinta a jihar.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na ƙasa ya fusata, ya yi magana kan yiwuwar ya yi murabus

Meyasa APC ta sauke shugabannin?

Da yake magana bayan ƙaddamar da kwamitin riƙon ƙwaryan, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa bai ji daɗin yadda al'amura suka taɓarɓare a jihar ba.

Ganduje ya bayyana cewa sun ɗauki matakin rushe shugabannin ne domin hana jam'iyyar rushewa a Benue.

Za a yiwa ɗan majalisar APC kiranye

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Ekimogun Roundtable ta ƴan asalin jihar Ondo ta fara shirin yin kiranye ga Abiola Makinde, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ondo Gabas/Ondo ta Yamma a majalisar wakilai.

Kungiyar ta yi zargin cewa ɗan majalisar na jam'iyyar APC ya yi watsi da aikinsa na majalisa ya koma ƙasar ketare ya samu waje ya yi zamansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng