Ministan Tinubu Ya Faɗi Gaskiya Kan Jita Jitar Yana Shirin Sauya Sheƙa

Ministan Tinubu Ya Faɗi Gaskiya Kan Jita Jitar Yana Shirin Sauya Sheƙa

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce zai ci gaba da zama a PDP ya tunkarin yakin da ke gabansa ba tare da tsoro ba
  • Wike ya kuma musanta raɗe-raɗin yana shirin sauya sheka zuwa APC mai mulki, inda ya ce ba zai bar jam'iyyar PDP ba
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da aka fara kiraye-kirayen a gaggauta korar Wike daga babbar jam'iyyar adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, ya sha alwashin ci gaba da zama a jam’iyyar PDP.

Ministan ya kuma musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirye-shiryen sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Wike ya yi maganar yiwuwar sasantawa kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Nyesom Wike ya ce ba zai bar jam'iyyar PDP ba a yanzu Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Wike na fama da rigima a Rivers

Matakin na Wike ya zo ne a daidai lokacin da ake gwabza fada tsakaninsa da Gwamna Fubara kan jagorancin jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas, The Nation ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC ne ya nada tsohon gwamnan jihar Ribas, Wike a matsayin ministan Abuja a bara watau 2023, rahoton Punch.

PDP: Wike ba zai canza jam'iyya ba

Mista Wike ya ce yana nan daram a PDP duk da adawar da Gwamna Siminalayi Fubara da wasu ƙusoshi ke nuna masa ciki ha da Atiku Abubakar.

Tsohon gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi ga ƴan jarida a ofishinsa bayan cika shekara guda da hawa kujerar ministan Abuja.

Wike na shirin komawa APC?

"Ba zan bar PDP ba duk tsananin faɗan da muke yi a gida (jihar Rivers) da kuma na kasa, zan ci gaba da gwabzawa har zuwa ƙarshe. Ban shirya shiga APC ba a yanzu.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na ƙasa ya fusata, ya yi magana kan yiwuwar ya yi murabus

"Na fada kuma zan sake maimaitawa, aikin da nake yi a nan shugaban ƙasa ne ya ba ni, kuma hankali na yana kansa domin sauke nauyin da aka ɗora mani.
"Amma ba zan naɗe hannu ina kallo jam'iyyar da na yiwa bauta tsawon shekaru, na sha baƙar wahala ta zo tana yi wa ƴaƴanta rashin adalci ba, ba zan lamurci haka ba."

- Nyesom Wike.

Shugaban PDP ya maida martani

Kuna da labarin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya ce yana nan daram babu wanda zai tsorata shi ya yi murabus daga muƙaminsa

Damagum ya nuna danuwa kan mutanen da ke ta surutu ba tare da sanin yadda ake tafiyar da harkokin kwamitin gudanarwa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262