Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Fusata, Ya Yi Magana kan Yiwuwar Ya Yi Murabus

Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Fusata, Ya Yi Magana kan Yiwuwar Ya Yi Murabus

  • Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya ce yana nan daram babu wanda zai tsorata shi ya yi murabus daga muƙaminsa
  • Damagum ya nuna danuwa kan mutanen da ke ta surutu ba tare da sanin yadda ake tafiyar da harkokin kwamitin gudanarwa ba
  • Ya ce masu sukarsa suna ƙara masa farin jini ne a wurin jama'a kuma har ya fara tunanin tsayawa takarar shugaban ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ya mayar da martani kan kiraye-kirayen da ake masa na ya yi murabus.

Umar Damagum ya bayyana cewa babu wata matsin lamba da za ta sa haka kurum ya yi murbaus daga matsayin shugaban PDP na ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana gaskiya kan jita jitar yana shirin sauya sheƙa daga PDP

Ambasada Umar Damagum.
Umar Damagun ya ce babu matsin lambar da zaj sa ya yi murabus daga shugabancin PDP Hoto: Umar Damagum
Asali: Twitter

Yadda jam'iyyar PDP ke fama da rigingimu

Punch ta tattaro cewa babbar jam'iyyar adawa PDP na shan fama da rikice-rikicen cikin gida kafin da kuma bayan babban zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu jiga-jigai da ƴaƴan jam'iyyar PDP na ganin Damagum na da hannu a rura wutar rikicin da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a jam'iyyar.

A ƴan kwanakin nan, kiraye-kiraye sun ƙaru kan shugaban PDP ya yi murabus domin jam'iyyar ta dawo kan hanya.

PDP: Umar Damagum ya maida martani

Yayin da yake mayar da martani a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja, Umar Damagum ya ce babu wanda zai ba shi tsoro ya sauka daga muƙaminsa.

Shugaban PDP ya yi wannan furucin ne a taron kaddamar da kwamitocin sulhu da ladabtarwa wanda Olagunsoye Oyinlola da Tom Ikimi za su jagoranta.

Damagum ya ce:

Kara karanta wannan

Mutum 2 ƴan gida sun mutu a wani mummunan ibtila'i da ya rutsa da su a Arewa

"Wannan saƙo ne ga dukkan masu ɗorawa Damagum laifi, Damagun kaza Damagun kaza, ku sani ba za ku iya tsoratar da ni ba, kuna ambatar sunana ina ƙara farin jini.

Shugaban PDP ya nuna damuwa

Ya kara da cewa sukar da ake yi masa ta sa ya kara farin jini har ma yana tunanin tsayawa takarar shugaban kasa saboda yadda sunansa ya yaɗu a wurin al'umma.

Damagum ya nuna damuwa game da mutanen da ba su san ayyukan kwamitin gudanarwa na kasa ba amma suna yada bayanan karya ga jama'a, cewar Daily Trust.

Jigon PDP ya buƙaci a kori Wike

A wani rahoton kuma ministan harkokin Abuja, Nyesom Ezonwo Wike na cigaba da shan kakkausar suka daga masu ruwa da tsakin jam'iyyar PDP.

Tsohon ministan na tarayya, Cif Edwin Clark ya bukaci a kori Nyesom Ezonwo Wike daga PDP domin ganin jami'yyar ta samu ci gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262