"Ba Zai Iya Ba," Malami Ya Bukaci Shugaba Tinubu Ya Tsige Minista 1 Nan Take
- Primate Elijah Babatunde Ayodele ya yi kira ga Shugaban Kasa ya kori ɗaya daga cikin ministocinsa idan yana son cimma burinsa
- Fitaccen limamin cocin ya ce Najeriya tana bukatar gogaggun mutane a matsayin waɗanda za su tafiyar da harkokin shugabanci
- Primate Ayodele ya buƙaci Bola Tinubu ya gaggauta ɗaukar mataki domin ceto ma'aikatar wasanni ta dawo kan turbar nasara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Shugaban cocin evangelical, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kori ministan wasanni, John Enoh.
Primate Ayodele ya kafa hujja da rashin tabuka abin kirki da tawagar Najeriya ta yi a gasar Olympics da aka yi a birnin Paris na kasar Faransa.
A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X, babban limamin cocin ya ce rashin ƙokarin Najeriya a Faris kaɗai ya isa ya sa a kori ministan daga aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya ta gaza taɓuka komai a Olympics
Idan ba ku manta ba, tawagar Najeriya ta gaza taɓuka abin kirki duk da sa ran da aka yi a kan ƴan wasan a karo na 19 da ta halarci gasar Olympics.
Bayan shafe kwanaki 16 ana fafatawa a gasar, Najeriya ta tashi hannu rabbana ba tare da cin wata lambar yabo ta a zo a gani ba a birnin Faris.
Ministan harkokin wasanni, John Enoh, wanda tsohon sanata ne a majalisa ta takwas ya jagoranci tawagar ƴan wasan Najeriya a gasar kuma shi aka ɗorawa laifi.
Ayodele ya ba Tinubu mafita
Da yake tsokaci kan rashin nasarar Najeriya a Faris, Primate Ayodele ya ce:
"Kamata ya yi Shugaba Tinubu ya kori ministan wasanni nan take. Ku tuna Najeriya ta kashe kimanin N12bn a gasar Olympics ta bana. Wannan kuɗin zai magance wasu matsalolin.
"A gaskiya, ya kamata su tsige ministan ba tare da ɓata lokaci ba, sannan a nemo wanda zai iya abin da ya dace a ɗora."
2027: Kwankwaso ya fara samun goyon baya
A wani rahoton kuma yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na gaba a 2027, Rabiu Kwankwaso ya fara samun cikakken goyon baya a NNPP.
Shugaban ƙungiyar ciyamomin NNPP na jihohin Najeriya, Tosin Adeyemi, ya ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su zaɓi nagartaccen shugaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng