Zaben Kano: Ana Kukan Ya Yi Tsada, KANSIEC Ta Fadi Dalilin Tsawwala Kudin Fom

Zaben Kano: Ana Kukan Ya Yi Tsada, KANSIEC Ta Fadi Dalilin Tsawwala Kudin Fom

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano ta kare matakin da ta ɗauka na sanya kuɗin fom domin tsayawa takara da ɗan karen tsada
  • Shugaban KANSIEC, ya bayyana cewa kuɗin komai yanzu a kasuwa ya tashi sannan za su kashe kuɗi sosai wajen shirya zaɓen
  • Ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya kan kuɗaɗen siyan fom ɗin domin ya riga da ya zama doka a wajen hukumar ta KANSIEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta ce babu gudu babu ja da baya kan kuɗin siyan fom domin takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe.

Hukumar dai ta ce masu son tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukuma za su biya N10m, yayin da ƴan takarar Kansila za su biya N5m kafin wa’adin ranar 18 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

NNPP ta yanke kudin tsayawa takara a zaben kananan hukumomin Kano

Za a fom na takara kan N10m a Kano
KANSIEC ta fadi dalilin sanya N10m a matsayin kudin fom Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Babu batun sauya kuɗin fom a Kano

Da yake magana game da ce-ce-ku-cen da sanarwar ta haifar, shugaban hukumar KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ya ce ba za a sauya kuɗin siyan fom ɗin ba, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa hukumar ta kasance mai zaman kanta kuma ta riga da ta yanke kuɗin da za a biya saboda haka babu gudu babu ja da baya kan lamarin, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Meyasa aka sa kuɗin fom da tsada?

"Ba za mu canza ko rage shi ba, babu gudu babu ja da baya. Ya ya riga ya zama doka a wajen mu."
"Ba wai domin a ƙarfafa yin siyasar kuɗi ba ne, komai a yanzu ba yadda yake ba ne a baya. Haka nan za mu kashe maƙudan kuɗaɗe."
"Kayayyaki da duk abin da za mu yi amfani da su dole za su ci kuɗi kuma mu za mu ɗauki nauyin kuɗin."

Kara karanta wannan

UBEC: Kano da wasu jihohi 3 a Arewa sun yi asarar tallafin sama da N4bn a 2023

"Mun faɗa a fili cewa hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya shafi kusan komai domin babu abin da ke da sauƙi yanzu a kasuwa."

- Farfesa Lawan Malumfashi

NNPP ta yanke kuɗin fom a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar NNPP a Kano ta yanke kuɗin siyan fom ga masu shawarar tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Jam'iyyar ta sanya N500,000 a matsayin kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙaramar hukuma, sai N150,000 na takarar Kansila, sai kuɗin na gani ina so N100,000 da N50,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng