Bayan Tinubu Ya Tafi Faransa, an Fara Maganar Korar Ministansa daga Jam’iyya

Bayan Tinubu Ya Tafi Faransa, an Fara Maganar Korar Ministansa daga Jam’iyya

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Ezonwo Wike na cigaba da shan kakkausar suka daga masu ruwa da tsakin jam'iyyar adawa ta PDP
  • Jigon 'yan hamayyar, Cif Edwin Clark ya bukaci a kori Nyesom Ezonwo Wike daga jami'yyar PDP domin ganin jami'yyar ta samu cigaba
  • Cif Edwin Clark ya yi kiran korar ministan na Abuja ne ga mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Iliyasu Damagun

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jigo a PDP kuma shugaban kungiyar PANDEF A Niger Delta, Cif Edwin Clark ya yi kira ga PDP ta kori ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike.

Cif Edwin Clark ya bayyana cewa korar ministan Abuja ce hanyar da za ta dawo da jam'iyyar PDP kan hanya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Cikin jam'iyyar APC ya ɗuri ruwa bayan kiran Jonathan ya tsaya takara a zaben 2027

Nyesom Wike
An bukaci a kori Wike daga PDP. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Cif Edwin Clark ya yi kiran ne ga mukaddashin shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin neman korar Wike a jam'iyyar PDP

Cif Edwin Clark ya bayyana cewa ba zai yiwu Wike na PDP ba amma kuma yana hada kai da jam'iyyar APC.

Clark ya kara da cewa abubuwan da Wike yake aikatawa suna kawo tasgaro ga PDP saboda haka ya bukaci a sallame shi daga jam'iyyar idan ana son PDP ta farfado.

Magana kan rikicin Wike da Fubara

Punch ta wallafa cewa Cif Edwin Clark ya kara da cewa daga cikin laifuffukan Wike akwai matsa lamba ga gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara.

Saboda haka Clark ya bukaci mukaddashin shugaban PDP, Umar Damagun da sakataren PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu su dauki mataki a kan Wike.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC, Ajaero ya yi fatali da gayyatar yan sanda, ya mika bukatunsa

Korar Wike: PDP ta kafa kwamitin sulhu

Jami'yyar PDP ta kafa kwamitin sulhu wanda Olagunsoye Oyinlola zai jagoranta da kuma kwamitin ladabtarwa da ke karkashin jagorancin Cif Tom Ikimi.

PDP ta kafa kwamitocin ne domin kawo karshen rikicin da ke cikin jam'iyyar kafin zaben shekarar 2027.

Wike ya yi kira a kori Atiku a PDP

A wani rahoton, mun ji cewa har yanzu rikicin da ke tsakanin Nyesom Wike da jiga-jigan jam'iyyar PDP na cigaba da ɗaukar zafi.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom wike ya yi kiran da a dakatar da Atiku Abubakar wanda hakan ya sanya ya sha caccaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng