Hantar Tinubu Ta Kaɗa, Matasa Sun Faɗi Abin da Zai Hana Atiku Karbar Mulki a 2027

Hantar Tinubu Ta Kaɗa, Matasa Sun Faɗi Abin da Zai Hana Atiku Karbar Mulki a 2027

  • Wata kungiyar matasa magoya bayan Atiku Abubakar a fara shirin tallata takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasar a 2027
  • Mai magana da yawun NYFA, Dare Dada ya ce babu wanda zai iya dakatar da Atiku Abubakar daga zama shugaban kasa na gaba
  • NYFA ta kuma soki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda ta ce sun gaza share hawayen ƴan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wata ƙungiyar magoya bayan Atiku Abubakar ta bayyana cewa Allah ne kaɗai zai iya dakatar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Nigerian Youths for Atiku (NYFA) ta ce babu wani ɗan adam da zai iya hana Atiku tsayawa takara da lashe zaɓen shugaban ƙasa na gaba a 2027.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, tsohon shugaban ICPC ta ƙasa ya riga mu gidan gaskiya

Atiku Abubakar da Tinubu.
Kungiyar matasa ta ce ba mai iya dakatar da Atiku a 2027 sai Allah Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Daraktan yada labarai na ƙungiyar NYFA, Mista Dare Dada, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Talata a Legas, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa sun fara shirin 2027

Dada ya ce ranar Asabar din da ta gabata kungiyar NYFA ta gana da shugabannin wasu kungiyoyin da suka fito daga jihohi sama da 28 domin fara shirin zaɓen 2027.

Ya ce wannan taron ya gudana ne a jihar Ekiti kuma sun tattauna abubuwan da suka shafi yadda za su tallata Atiku ya yi nasara.

"Allah ne kaɗai zai iya dakatar da Atiku daga zama shugaban ƙasa na gaba a 2027," in ji kakakin NYFA.

NYFA: 'Atiku ne shugaban ƙasa na gaba'

Mista Dare Dada ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta yi duk mai yiwuwa wajen jawo hankalin matasan Najeriya su kaɗawa Atiku Abubakar ƙuri'unsu.

A cewarsa, suna da ƙwarin guiwar Atiku Abubakar zai lallasa dukkan ƴan takara ya zama shugaban ƙasa a 2027 domin gina shugabanci na gari a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya faɗi gaskiya kan jita jitar yana shirin sauya sheƙa

Kungiyar matasan ta soki salon Tinubu

Kakakin NYFA ya ce a bayyane yake gwamnatin APC ta gaza share hawayen ƴan Najeriya musamman halin matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Dada ya sake nanata kiran da kungiyar ta yi ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya sake nazari kan wasu manufofinsa domin magance matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Wani masoyin Atiku kuma ɗan PDP a Katsina, Kabir Anyalo ya ce ba gudu ba ja da baya, Atiku za su yi sak a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Jigon PDP ya shaidawa Legit Hausa cewa duk da ana ta kiran ya hakura haka nan, amma su kam sun shirya, za su marawa wazirin Adamawa baya ko sau 100 zai fito takara.

"Har yanzu ina ganin Atiku ne kaɗai mafita a Najeriya, amma yanzu lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su sauka daga motar APC.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi zazzafan martani ga Shugaba Tinubu kan dawo da tallafin man fetur

"Muna fatan idan Allah ya so kamar yadda ƴan uwanmu matasa suka faɗa, babu wani indai ɗan adam ne da zai iya dakatar da Atiku a 2027," in ji Kabiru.

Atiku Abubakar ya soki Bola Tinubu

A wani rahoton kuma Alhaji Atiku Abubakar ya soki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan ci gaba da biyan tallafin man fetur a Najeriya.

Tsohon mataimakin shugabn ƙasar ya ce bayanan da ke fitowa sun ƙara nuna akwai tufka da warwara da shakku a gwamnati mai ci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262