Atiku Ya Yi Zazzafan Martani ga Shugaba Tinubu kan Dawo da Tallafin Man Fetur

Atiku Ya Yi Zazzafan Martani ga Shugaba Tinubu kan Dawo da Tallafin Man Fetur

  • Alhaji Atiku Abubakar ya soki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan ci gaba da biyan tallafin man fetur a Najeriya
  • Tsohon mataimakin shugabn ƙasar ya ce bayanan da ke fitowa sun ƙara nuna akwai tunfa da warwara da shakku a gwamnati mai ci
  • Wazirin Adamawa ya ce NNPCL na ƙarawa ƴan Najeriya wahalhalu bayan waɗanda su ke fama da su na hauhawar farashin kayayyaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubajar ya soki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan dawo da tallafin man fetur.

Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023 a inuwar PDP, ya ce akwai shakku da ayar tambaya kan ingancin gwamnati mai ci.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan umurnin Tinubu na maido tallafi duk da ana sayen fetur a N900

Atiku Abubakar da Tinubu.
Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Tinubu kan rahoton biyan tallafin fetur Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tun farko dai kun ji cewa Shugaba Tinubu ya amince da buƙatar kamfanin mai na kasa NNPCL ya yi amfani da ribar 2023 wajen biyan tallafin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya caccaki Bola Tinubu

Da yake mayar da martani kan lamarin a shafinsa na X, Atiku ya ce hakan ya ƙara fito da tsantsar rashin gaskiyar gwamnatin Tinubu.

Atiku ya ce wannan rahoton ya nuna Shugaban kasa Bola Tinubu ba dattijo mai magana ɗaya ba ne domin furucinsa na cin karo da ayyukansa.

"Tufka da warwara tsakanin kalaman shugaban kasa da kuma ayyukansa sun zubar da mutunci da jefa shakku kan gaskiyar gwamnatinsa.
"A lokacin da ƴan Najeriya ke fama da matsanancin karancin mai da tsadar wutar lantarki, jinkirin gyara matatar Fatakwal abin kunya ne.
"Hakan gazawa ce da ta rataya a wuyan Shugaba Tinubu tun da shi ne ministan albarkatun man fetur."

Kara karanta wannan

Tinubu ya fara daukar matakin tsuke bakin aljihun gwamnati

- Atiku Abubakar.

Atiku ya ɗora laifi kan NNPCL

Atiku ya kuma koka kan yadda kamfanin NNPCL ke ƙara jefa ƴan Najeriya cikin wahala duk da ƙuncin da suke ciki sakamakon ƙarancin man fetur da hauhawar farashi.

Wazirin Adamawa ya bukaci Bola Tinubu ya shiga tsakani domin warware rigingimun matatar Ɗangote da masu shigo da mai, inda ya ce shiru ba na shi ba ne.

Tinubu ya ba shugaban izala muƙami

Kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugaban Izala reshen Kano, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai, NAHCON.

Shugaban ƙasar ya yi wannan naɗi ne bayan ya tsige Jalal Arabi, wanda EFCC ke bincika kan zargin karkatar da kuɗin tallafin hajjin bana 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262