Tinubu: Babban Jigo Ya Hango Wanda Ƴan Najeriya Za Su Jefawa Ƙuri'u a 2027

Tinubu: Babban Jigo Ya Hango Wanda Ƴan Najeriya Za Su Jefawa Ƙuri'u a 2027

  • Kwamared Adegoke Alawuje ya ce duk da wahalar da ƴan Najeriya ke ciki za su sake zaɓen Bola Ahmed Tinubu a 2027
  • Babban jigon na APC kuma shugaban kungiyar magoya bayan Tinubu ya ce halin da Najeriya ke ciki na ɗan lokaci ne
  • Ya kuma roki ƴan Najeriya su kara hakuri da juriya domin nan ba da jimawa ba za su ga haske a karkashin mulkin nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigon jam'iyyar APC, Kwamared Abdulhakeem Adegoke Alawuje ya ce duk da wahalar da ake sha yana da yaƙinin ƴan Najeriya za su sake zaɓen Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Kwamared Alawuje, kodinetan kungiyar magoya bayan Tinubu 'Disciples of Jagaban' ya roƙi mutane su kara hakuri da Shugaba Tinubu kan tsadar rayuwar da ake ciki.

Kara karanta wannan

'Yan bindigar da suka sace ɗaliban jami'o'i 2 a Arewa sun turo saƙo, sun faɗi buƙatarsu

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Jigon APC ya yi hasashen ƴan Najeriya za su amince da tazarcen Tinubu a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wahala za ta zo karshe a mulkin Tinubu

Ya ce nan ba da jimawa ba wahalar da mutane ke sha za ta kau kuma ƴan Najeriya da kansu za su fara rokon Bola Tinubu ya nemi tazarce a 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, kamar yadda The Nation ta tattaro.

Jigon APC ya ba ƴan Najeriya haƙuri

"Radadin da ƴan Najeriya ke ciki a halin yanzu na dan lokaci ne, kuma idan suka ƙara hakuri, za su ji daɗi a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu.
“Zan iya ba ku tabbacin cewa nan gaba ‘yan Nijeriya za su nemi Tinubu ya ci gaba da mulki har bayan 2027 saboda wannan kebur da ake sha na ɗan lokaci ne.
“Duk da haka, ina rokon al'ummar ƙasar nan su ci gaba da zama masu haƙuri da juriya na ɗan kankanin lokaci domin nan gaba kaɗan tsadar rayuwa za ta zama tarihi."

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 2 da aka ƙulla da nufin wargaza shirin tazarcen Bola Tinubu a 2027

- Abdulhakeem Adegoke Alawuje.

Alawuje ya aika saƙo ga matasa

Jigon APC ya ƙara da yin kira kira ga matasan Najeriya ka da su bari wasu bara gurbin ‘yan siyasa masu son rai su rude su ko su jirkita masu tunani.

Kwamared Alawuje ya baygana cewa kamata ya yi talakawa su ɗauki Shugaba Tinubu a matsayin aboki, ka da su bari wasu maƙiya su shiga tsakaninsu.

Ganduje ya magantu kan takara a 2027

A wani labarin kuma Shugaban APC Abdullahi Ganduje ya musanta raɗe-raɗin yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

Ganduje, tsohon gwamnan Kano ya ce fastocin da ke yawo ba su da alaƙa da shi kuma ya yi zargin akwai hannun wasu ƴan Kwankwasiyya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262