PDP v APC: Kotun Koli Ta Shirya Yin Hukunci a Shari’ar Neman Tsige Gwamna
- Kotun Koli ta tanadi hukunci a takaddamar da ta dabaibaye zaben gwamnan jihar Bayelsa da hukumar INEC ta gudanar a 2023
- Jam'iyyar APC da dan takararta Timipre Sylva sun shigar da kara a Kotun Kolin suna kalubalantar hukuncin kotuna biyu
- A ranar Litinin, Kotun Kolin mai kwamitin alkalai biyar ta jingine hukunci tare da sanar da bangarorin biyu matakin gaba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Litinin, 19 ga watan Agusta, kwamitin alakali biyar na Kotun Koli, ya tanadi hukunci shari'ar zaben gwamnan Bayelsa.
Kotun Kolin ta shirya yanke hukunci a wannan zama, bayan sauraron bangarorin da abin ya shafi a karar da Timipre Sylva na APC ya shigar.
Bayelsa: Hukuncin Kotun Kolin ranar Litinin
Sylva da jam'iyyarsa ta APC sun kalubalanci sanarwar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) kan sakamakon zaben gwamna na 2023 a jihar, inji rahoton AIT News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai a wani hukunci da ta yanke a ranar Litinin, Kotun Kolin ta ce ta jingine yanke hukunci kan karar da aka shigar.
Channels TV ta rahoto cewa Kotun kolin ta sanar da bangarorin biyu cewa za ta tura masu sako na ranar da ta tsayar domin yanke hukuncin karshe kan shari'ar.
Sylva ya kalubalanci nasarar gwamna Diri
Sylva a watan Mayu, ya nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben gwamna a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Julius Bokoru ya fitar.
Kotun zabe ta yanke hukuncin ne ranar 17 ga Mayu, 2024, a Abuja, inda ta tabbatar da nasarar zaben Diri da mataimakinsa, Sanata Lawrence Eruwjadkpo.
Sylva da APC sun daukaka kara; sai dai a watan Yuli, kotun daukaka kara ta Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar na kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben Bayelsa.
Kotu ta tanadi hukunci a zaben gwamnan Kogi
A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa Kotun Koli ta tanadi hukunci kan karar da jam'iyyar SDP da dan takararta suka shiga kan zaben gwamnan jihar Kogi.
Kotun Kolin ta jingine hukunci kan shari'ar bayan bangarorin da abin ya shafa suka kammala gabatar da jawabai, a shari'ar kalubalantar nasarar zaben Gwamna Ahmed Usman Ododo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng