Ganduje Ya Yi Maganar Neman Takarar Shugaban Ƙasa a 2027, Ya Zargi Ƴan Kwankwasiyya
- Shugaban APC Abdullahi Ganduje ya musanta raɗe-raɗin yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027
- Ganduje, tsohon gwamnan Kano ya ce fastocin da ke yawo ba su da alaƙa da shi kuma ya yi zargin akwai hannun wasu ƴan Kwankwasiyya
- Tun farko dai fastocin Ganduje tare da kuma gwamnan jihar Imo a matsayin abokin takararsa sun ja hankali a soshiyal midiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nesanta kansa da fastocin takarar shugaban ƙasa da ke yawo a soshiyal midiya.
Ganduje ya musanta raɗe-raɗin cewa yana shirin fitowa takarar shugaban ƙasa tare da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma a babban zaɓen 2027.
Shugaban APC ya ƙaryata lamarin ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Edwin Olofu ya fitar, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda fastocin Ganduje suka yaɗu
Fastocin Ganduje da Uzodinma a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa sun bazu a kafafen sada zumunta, inda ake raɗe-raɗin zai gwabza da Tinubu a APC.
Amma Ganduje ya ce babu kanshin gaskiya a jita-jitar kuma ya yi zargin cewa da yiwuwar wasu ƴan kwankwasiyya ne suka shirya makircin domin haɗa shi faɗa da Bola Tinubu.
Ganduje ya zargi ƴan Kwankwasiyya
A sanarwar, Olufo ya ce:
"Muna sanar da ƴan Najeriya cewa fastocin da ke yawo a soshiyal midiya masu ikirarin shugaban APC Ganduje zai shiga takarar shugaban ƙasa a 2027 tare da gwamnan Imo a matsayin abokin takara ƙarya ne.
"APC na tabbatarwa mutane cewa wannan makirci ne na wasu ɓata gari, mai yiwuwa da hannun wasu yan Kwankwasiyya, waɗanda suka kudiri aniyar lalata alaƙar Ganduje da shugaban kasa, Bola Tinubu.
- Jam'iyyar APC
Ganduje na shirin gwabzawa da Tinubu?
Edwin Olofu ya ƙara da cewa Ganduje na nan a matsayin mai biyayya ga shugaban ƙasa kuma ya maida hankali wajen taimaka masa ya cika manufofinsa.
A ƙarshe ya yi kira ga ƴan Najeriya su yi fatali da irin waɗannan kagaggun labarin kuma su guji yaɗa labaran da ba su da tushe, rahoton Vanguard.
Tinubu zai gana da matasan Najeriya
A wani rahoton Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da matasan Najeriya har 3,000 domin tattaunawa kan kawo cigaba.
Shugaban matasan jam'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ne ya fitar da sanarwa kan yadda taron zai gudana a fadar shugaban kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng