Zaben 2027: Fastocin Takarar Shugaban Kasa na Ganduje Sun Mamaye Soshiyal Midiya
- Hotunan fastocin neman takarar shugaban kasa na Abdullahi Ganduje da Hope Uzodinma sun mamaye shafukan sada zumunta
- Fastocin sun nuna cewa Ganduje zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027, yayin da Uzodinma zai kasance mataimakinsa
- Sai dai Ganduje ya yi martani kan wadannan fastoci inda ya ce wasu bata gari ne kawai ke son hada shi fada da Shugaba Bola Tinubu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Fastocin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da gwamnan Imo, Hope Uzodinma, na neman takarar shugaban kasa a shekarar 2027, sun yadu a soshiyal midiya.
Fastocin sun nuna cewa Ganduje wanda shi ne shugaban APC na kasa a yanzu zai tsaya takarar shugaban kasa, yayin da Uzodinma zai kasance mataimakinsa.
Jaridar Daily Trust ta ce fastocin da ke dauke da taken, ‘Ga ‘yan Najeriya, wadata da ci gaban al'umma’ sun kuma nuna cewa ‘yan siyasar biyu za su fafata a zaben 2027 a karkashin APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC: Ana kishin kishin din cire Ganduje
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wata jita-jita ke ta yawo cewa ana yunkurin cire Ganduje daga mukaminsa na shugaban APC na kasa domin ba shi mukamin jakadanci.
Sai dai tuni kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa (NWC) ya bayyana cewa wannan jita jitar ba gaskiya ba ce, labarin karya ne kawai ake yadawa.
Ganduje ya sha fadin cewa Shugaba Tinubu zai sake neman wa’adi na biyu kuma zai ci zabe a karo na biyu, amma bayyanar fastocin ya sabawa ikirarinsa.
Ganduje ya magantu kan bayyanar fastocin
Da yake mayar da martani, Ganduje ya bayyana fastocin a matsayin aikin wasu bata gari da kuma marubutan karya da ke son cimma wata manufa ta su.
Mista Edwin Olofu, babban sakataren yada labaran Ganduje, a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai ya ce, “abin dariya ne, wasan yara da kuma son bata suna."
Ya kara da cewa:
“Aikin wasu baragurbin marubuta jarida ne, su ne dai wadanda suke ta yada jita-jitar cire shi (Ganduje) daga matsayin shugaban APC na kasa.
“Wannan shiri ne da aka yi shi da gangan domin haifar da rashin jituwa tsakaninsa da dan uwansa kuma jagoransa, Bola Ahmed Tinubu."
"Muna tare da Ganduje" - Shugabannin APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugabannin APC na jihohin36 da Abuja sun kada kuri’ar gamsuwa da shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje.
A cewarsu ba za su zuba ido suna kallo a ci mutuncin shugaban na APC kamar yadda aka yi wasu shugabannin APC da suka gabata ba.
Asali: Legit.ng