Shiri Ya Baci: Mataimakin Gwamna Ya Yi wa Gwamnan PDP Tonon Silili

Shiri Ya Baci: Mataimakin Gwamna Ya Yi wa Gwamnan PDP Tonon Silili

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya fito ya yi magana kan irin taimakon da ya yiwa Gwamna Godwin Obaseki na jihar
  • Philip Shaibu ya bayyana cewa da kuɗinsa ya sanya gwamnan ya lashe zaɓe saboda lokacin da ya fito takara ba shi da ko kwaɓo
  • Ya bayyana cewa saɓanin abin da wasu ke cewa na gwamnan ne ya sa aka san shi a siyasance, shi ne ya taimaki gwamna har aka san shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya ƙaryata batun cewa Gwamna Godwin Obaseki ne ya sa aka san shi a siyasance.

Philip Shaibu ya bayyana cewa shi ne ya yiwa gwamnan rana a siyasance.

Kara karanta wannan

Sace takardun shari'a: Ganduje ya yi wa Gwamna Abba martani mai zafi

Philip Shaibu ya caccaki Gwamna Obaseki
Mataimakin gwamnan Edo ya caccaki Gwamna Godwin Obaseki Hoto: Philip Shaibu, Godwin Obaseki
Asali: UGC

Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne yayin hira da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Philip Shaibu ya taimaki Gwamna Obaseki

Philip Shaibu ya ce nemansa aka yi domin ya zama abokin takarar Obaseki a zaɓen 2016 saboda ya ɗaga darajar tikitin takarar.

A cewarsa, Gwamna Obaseki a lokacin ba shi da ƙwarewa a siyasance da kuma kuɗi domin tsayawa takara.

"Mu muka sanya Obaseki ya zama gwamna. Obaseki ba ɗan siyasa ba ne, kuma Obaseki bai da kuɗin da zai iya tsayawa takara."
"Oshiomhole ne ya kawo shi, lokacin da Oshiomhole ya kawo shi, wasu daga cikin mu sun bayyana cewa ba shi ya kamata a tsayar ba."
"Sai da Oshiomole ya ɗauki watanni uku sannan ya shawo kan wasu daga cikin magoya bayanmu da ni kaina domin mu goyi bayan Obaseki."

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

Lokacin da muka yanke shawarar mara masa baya saboda girmama Oshiomole da muke yi, Obaseki bai kawo ko kwabo ba. Mu da abokanmu muka samar da kuɗi domin ya zama gwamna."

- Philip Shaibu

Philip Shaibu ya koma bakin aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Edo da aka mayar kan mulki, Kwamared Philip Shaibu, ya koma bakin aikinsa ranar Litinin.

Hakan na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya ta soke matakin majalisar dokokin jihar Edo na tuge Shaibu, ta umarci ya koma kan muƙaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng