Gwamna Abba Ya Naɗa Manjo Janar na Sojoji a Shirgegen Muƙamin Gwamnati a Kano
- Gwamna Abba Kabir ya naɗa Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya a matsayin sabon kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida
- Abba Kabir ya sanar da wannan naɗin ne a wurin rantsar da majalisun gudanarwa da jami'o'i da manyan makarantu na jihar Kano
- Ya buƙaci M.I Idris da ya yi amfani da gogewarsa ta sojoji wajen inganta sha'anin tsaro da zaman lafiya a faɗin jihar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya naɗa Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya) a matsayin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida.
Kimanin watanni biyar da suka gabata Gwamna Abba Kabir ya kirkiro ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida a Kano amma bai naɗa kwamishina ba a lokacin.
Gwamnan ya sanar da naɗin sabon kwamishinan ne a wurin bikin rantsar da majalisun gudanarwa na manyan makarantun Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya naɗa kwamishinan tsaro
Hakan na kunshe a wani faifan bidiyo da shafin Kwankwason Tuwita ya wallafa a manhajar X wanda aka fi sani da Twitter da yammacin ranar Jumu'a.
Ana sa ran naɗin tsohon babban jami'in sojan zai ƙara inganta tsaron cikin gida a Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
"Na amince da naɗin Manjo Janar M. I Idris (Mai ritaya) a matsayin kwamishina kuma mamban majalisar zartaswa ta jihar Kano.
"Bayan haka ina sanar da cewa zai jagoranci sabuwar ma'aikatar tsaron cikin gida," in ji Gwamna Abba.
Gwamnan Kano ya ja hankalin sabon kwamishinan
Gwamna ya buƙaci Manjo Janar Idris mai ritaya da ya tunkari ayyukan da ya rataya a wuyansa da kwazo da fasaha irin wanda ya nuna a lokacin aikinsa na soja.
Abba Kabir ya kuma nanata muhimmancin sabuwar ma'aikatar na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a faɗin jihar Kano.
Gwamna Abba ya gana kungiyar Qatar
A wani rahoton kuma gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta gana da kungiyar kasar Qatar mai ba al'umma tallafi a fadin duniya.
Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara ga kungiyar ne domin samar da hanyoyin yaki da talauci da inganta ilimi a Kano baki daya.
Asali: Legit.ng