Jihar Kudu Ta Nemi Daukin Shugaban APC Ganduje domin Ceto Siyasar Tinubu a 2027

Jihar Kudu Ta Nemi Daukin Shugaban APC Ganduje domin Ceto Siyasar Tinubu a 2027

  • Matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya sa wasu yankunan kasar nan sun fara neman daukinsa
  • Kungiyar kishin APC a jihar Enugu ta nemi Ganduje ya gaggauta shiga tsakani domin warware barazanar masu cin amanar jam'iyyar
  • Kungiyar ta ce matukar Dakta Abdullahi Ganduje bai kai daukin ba, akwai babbar barazana ga nasarar shugaba Bola Tinubu a 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu - Kungiyar Civil Society Coalition for Transparency ta nemi daukin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje a jihar Enugu.

Kungiyar ta yi koken cewa wasu daga cikin 'yan jam'iyyar na yi wa APC a jihar zagon kasa, kuma taimako Ganduje ne kawai zai fitar da su daga barazanar.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Fastocin takarar shugaban kasa na Ganduje sun mamaye soshiyal midiya

Ganduje
An nemi daukin shugaban APC, Abdullahi Ganduje gabanin 2027 Hoto: Ganduje TV
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Hon. Mike Femi ya zargi wasu jiga-jigan APC a Enugu da cin amanar jam'iyyar da sauran ayyuka da za su kai ta kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Mike ya kara da cewa su na sane da yadda wasu ke shirin jefa APC a matsala kafin zaben 2027.

An roki Ganduje ko Tinubu ya samu cikas

Shugaban kungiyar Civil Society Coalition for Transparency ya bayyana cewa zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu zai fuskanci kalubale.

Shugaban kungiyar, Mike Femi ne ya bayyana haka a rokon da ya yiwa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje na neman dauki a jihar Enugu.

Hon. Femi ya ce idan har aka yi wasa, manakisar wasu manyan 'yan jam'iyyar za ta kai Tinubu kasa a zaben 2027 da ake sa ran zai fito takara karo na biyu, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 2 da aka ƙulla da nufin wargaza shirin tazarcen Bola Tinubu a 2027

APC ta musanta shirin sauke Ganduje

A wani labarin kun ji cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta bayyana cewa babu gaskiya a cikin labarin da ke cewa ana shirye-shiryen sauke shugabanta, Abdullahi Ganduje.

APC ta fadi haka ne biyo bayan labarin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Dr. Ganduje tayin jakada domin saukaka tsige shi daga mukaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.