Kashim Shettima Ya Tono Sirri a Rayuwar Tinubu, Ya Bar Mutane da Mamaki
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana wasu abubuwan da suka shafi rayuwar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Kashim Shettima ya bayyana irin kokarin da Bola Tinubu yake wajen ganin ya farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya domin samun cigaba
- Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin taron ƙaddamar da wani littafi a birnin tarayya Abuja a yammacin jiya Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin mutum mai gudun duniya.
Kashim Shettima ya bayyana irin abincin da suka ci a lokacin da suka kai ziyara gidan Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Kashim Shettima ya ce Bola Tinubu ya mayar da hankali kan farfaɗo da tattalin Najeriya a halin yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Labarin cin abinci a gidan Bola Tinubu
Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa wata rana sun je gidan Bola Tinubu a Legas aka karrama su da nau'ukan abinci daban daban kuma gidansa na Maiduguri ya fi na Tinubu kyau.
Shettima ya ce amma babban abin mamaki Bola Tinubu bai ci abincin ba sai dai garin kwaki da gyada ya sha.
Shettima ya ba da labarin agogon Tinubu
Punch ta wallafa cewa Kashim Shettima ya bayyana cewa tun da ya hadu da Bola Tinubu yana amfani da agogon hannu ne guda daya.
Saboda haka ya nuna cewa rayuwar Bola Tinubu a cike take da zuhudu da ya kamata yan Najeriya su yarda da shi wajen ba su amanar ƙasar nan.
Ƙoƙarin Tinubu na farfaɗo da tattali
Kashim Shettima ya ce a yanzu haka Bola Tinubu ya karkata kan farfaɗo da tattalin Najeriya ne ba neman duniya ba.
Ya kuma yi bayyana cewa ko da Atiku Abubakar ko Peter Obi ne suka samu mulki za su cire tallafin mai domin farfaɗo da tattalin Najeriya.
2027: An gargadi yan Arewa kan Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar Yarabawa ta yi magana kan masu neman sojoji su karbe mulkin Najeriya daga hannun Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kungiyar, Hammed Olalekan ya ce mulkin Najeriya na kowa da kowa ne kuma ya fadi yadda suke fata zaben 2027 ya kasance.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng