Karamar Magana Ta Zama Babba Yayin da APC Ta Tabo Batun Tsige Ganduje

Karamar Magana Ta Zama Babba Yayin da APC Ta Tabo Batun Tsige Ganduje

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta yi martani kan rahotannin da ke yawo dangane da shirin tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancinta
  • Mataimakin sakataren jam'iyyar na ƙasa, Barista Fetus Fuanter, ya yi watsi da rahotannin inda ya ce babu ƙamshin gaskiya a cikinsu
  • Fetus Fuanter ya kuma bayyana cewa APC ba ta da masaniya kan batun cewa ana shirin ba tsohon gwamnan na jihar Kano muƙamin jakada

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai shirin maye gurbin Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Wannan martanin ya biyo bayan rahotannin da ke nuni da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya naɗa Ganduje a matsayin jakada, domin ya samu sauƙin tsige daga matsayin shugabancin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasa, tsofaffin hadiman Ganduje sun kafa kungiya da manufa 1 a Kano

APC ta yi martani kan batun tsige Ganduje
APC ta musanta batun tsige Ganduje Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Martanin APC kan batun tsige Ganduje

Sai dai bayan taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa (NWC) a Abuja ranar Alhamis, mataimakin sakataren jam’iyyar na ƙasa Barista Fetus Fuanter, ya musanta batun raba Ganduje da shugabancin APC, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Festus Fuanter ya bayyana cewa babu wani shiri na tsige Ganduje kuma jam’iyyar ba ta da masaniya kan wani shirin naɗa shi a matsayin jakada da ake yi.

Jam'iyyar APC za ta yi taron NEC

Mataimakin sakataren ya kuma bayyana cewa jam’iyyar APC ta shirya taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) a ranar 12 ga watan Satumba.

Wannan dai shi ne taron kwamitin zartarwa na ƙasa na farko da jam'iyyar za ta yi tun bayan da Ganduje ya karɓi ragamar shugabancinta a ranar 3 ga watan Agustan 2023.

Kwamitin NEC shi ne na biyu mafi girma da yake yanke hukunci a jam’iyyar, bayan babban taro na ƙasa.

Kara karanta wannan

Sace takardun shari'a: Ganduje ya yi wa Gwamna Abba martani mai zafi

Bugu da ƙari, Fuanter ya bayyana cewa za a yi taron manyan ƙusoshin APC na ƙasa a ranar 11 ga watan Satumba, kwana ɗaya kafin taron na NEC.

Ganduje ya caccaki Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da mayar da mulki wani babban abin dariya.

Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan iƙirarin gwamnan na cewa an sace takardun kotu na shari'ar da ake yi masa kan zargin cin hanci da rashawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng