Zaben Ondo: Cikin Ganduje Ya Kada, Gwamnan PDP Ya Ba da Lakanin Kayar da APC
- Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan Ondo na jam'iyyar PDP
- Gwamna Adeleke ya nunawa ɗan takarar PDP, Agboola Ajayi, dabarar da ya yi amfani da ita wajen kayar da APC a jihar Osun
- Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin jam'iyyar da su bi lungu da saƙo domin nemo waɗanda za su kaɗa ƙuri'a ga ɗan takarar PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce ya ba ɗan takarar gwamnan jihar Ondo na PDP, Agboola Ajayi, dabarun da zai yi amfani da su wajen lashe zaɓen jihar Osun.
Gwamna Ademola Adeleke shi ne shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP na ƙasa a zaben gwamnan jihar Ondo.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen PDP zai fara aiki
Gwamna Adeleke ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP a jihar a birnin Akure, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Adeleke ya kuma bayyana cewa al'ummar jihar su ne ke da ikon samar da wanda zai yi nasara a zaɓen na ranar, 16 ga watan Nuwamban 2024.
Gwamna Adeleke ya yi wa APC shaguɓe
"Kafin mu hau gwamnati, sun ce ba za mu iya yin komai ba a jihar Osun. Yanzu a koma jihar a gani, abin da jam’iyyar APC ta kasa cimmawa a cikin shekaru 12, mun yi shi a ƙasa da shekara daya da rabi."
"Jama'a su ne za su yanke hukuncin wanda zai zama gwamna a cikin ƴan takarar da ke fafatawa a zaɓen."
"Babu batun yin dabanci. Za mu yi yaƙin neman zaɓe ne kan abubuwan da za mu yi. Mutane za su yanke hukunci. Ku koma yankunanku ku tallata PDP ga jama'a."
- Gwamna Ademola Adeleke
Gwamnan ya kuma buƙaci ƴan jam'iyyar da su bi lungu da saƙo domin nemowa Agboola Ajayi mutanen da za su kaɗa masa ƙuri'a.
Ƴan APC sun koma PDP a Ondo
A wani labarin kuma, kun ji cewa mambobin an jam'iyyar APC mai mulki fiye da 1000 a ƙaramar hukumar Akure ta Kudu sun sauya sheƙa zuwa PDP jihar Ondo.
Masu sauya sheƙar ƙarƙashin jagorancin Mayowa Ajemoju Boboye sun bayyana rashin bai wa kowa haƙƙinsa a matsayin dalilin barin APC mai mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng