Tsohon Gwamnan Kano Ya Faɗi Gaskiyar Yadda Ya Yi da Kuɗin Ƙananan Hukumomi

Tsohon Gwamnan Kano Ya Faɗi Gaskiyar Yadda Ya Yi da Kuɗin Ƙananan Hukumomi

  • Malam Ibrahim Shekarau ya ce har ya sauka daga mulkin jihar Kano bai taɓa ko sisi daga kuɗin kananan hukumomi ba
  • Tsohon gwamnan ya ce babu wani ɗan kwangila da ya taɓa zama da shi da nufin a ware masa lada ko kaso daga kuɗin aiki
  • Shekarau ya faɗi haka a taron manema labarai gabanin fara bikin cika shekaru 70 da kafa kungiyar ɗalibai musulmi MSSN

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa bai taba ɗaukar ko sisi daga cikin kuɗin kananan hukumomi ba har ya bar mulki.

Haka nan kuma Malam Shekarau ya ce tsawon shekaru takwas da ya shafe a kujerar gwamnan Kano, bai taɓa neman wani kaso ko lada daga ƴan kwangila ba.

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasa, tsofaffin hadiman Ganduje sun kafa kungiya da manufa 1 a Kano

Malam Ibrahim Shekarau.
Shekarau ya yi ikirarin bai taɓa cin ko Naura daga kason kuɗin kananan hukumomin Kano ba Hoto: Mallam Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai gabanin bikin cika shekaru 70 na kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya (MSSN).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekarau shi ne shugaban kwamitin shirya bikin cika shekaru 70 na ƙungiyar dalibai musulmi ta ƙasa MSSN, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yadda MSSN ta taimakawa Shekarau

Tsohon gwamnan dai ya alaƙanta wannan gaskiya da rikon amana da ya nuna da tasirin shigarsa MSSN tun wuri.

Sanata Shekarau bayyana cewa shiga cikin ƙungiyar tun yana ɗan shekara 19 ya taimaka masa wajen zama mutum mai gaskiya da kamala.

"Ban taɓa zama muka yi yarjejeniyar wani kaso da ɗan kwangila ba, a ko da yaushe ƙalubalantar su nake, idan kuma akwai ɗan kwangilar da muka yi aiki tare a shekaru takwas kuma na nemi na goro to ya fito ya yi magana."

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

Shekarau ya taɓa ɗaukar kudin kananan hukumomi?

Shekarau ya ƙara nanata cewa babu wani kwamishina ko shugaban ƙaramar hukuma da ya taɓa kawo masa kudi haka kurum, rahoton The Nation.

Ya kuma kara jaddada cewa ko da wasa bai taɓa karkatar da kason kuɗin kananan hukumomi da ake turowa daga tarayya ba.

Gwamna Abba ya koka da mulkin Ganduje

Kuna da labarin gwamnatin jihar Kano ta bayyana damuwa kan yadda aka samu cin hanci fiye da ko yaushe a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Ganduje ya kassara jihar musamman wurin cin hanci da rashawa wanda ya yi muni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262