Sanatan Kaduna Ya Kara Tone Tone, Ya Faɗi Makudan Kudin da Ake Ba Sanatoci a Wata
- Sanata Shehu Sani ya kara nanata kalamansa kan adadin kudin da ake biyan kowane sanata duk wata a Najeriya
- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya yi wannan magana ne bayan hukumar RMAFC ta fitar da kudin 'yan majalisa
- A ƴan kwanakin nan dai ana surutu a kan makudan kuɗin da gwamnatin tarayya take biyan ƴan majalisa na ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Yayin da ake ta surutu kan adadin kudin da ake biyan ƴan majalisar tarayya, Shehu Sani ya ce N13m aka rika biyansu duk wata a majalisa ta takwas.
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewa a yanzu kuwa sanatocin majalisa ta 10 suna karɓar N21m a kowane karshen wata.
Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na manhajar X yayin da yake martani ga ikirarin hukumar tattara kuɗaɗen shiga RMAFC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
RMAFC ta faɗi albashin sanatoci
RMAFC ta bayyana cewa kowane sanata na samun Naira miliyan guda a matsayin albashinsa na wata.
Sanata Shehu Sani ya jaddada cewa hukumar RMAFC na kokarin ɓoye gaskiya ne kawai amma alƙaluman da ta bayyana ba haka suke ba.
Sanata Shehu Sani ya maida martani
"Na yi sanata kuma na san abubuwan da suka faru a lokacin da muke mulki da kuma wanda ke faruwa a yanzu. Hukumar RMAFC tana wasa ne da alkaluma.
"A gefe guda ta ƙebe albashin da ake biyan sanatoci, sannan kuma ta jero alƙaluman yadda kowane sanata ke samun N20m a shekara huɗu.
"Na ga kalaman Sanata Kawu Sumaila daga Kano, wanda ya tabbatar da abin da na faɗa dangane da albashin sanatoci musamman karɓar N21m a kowane wata."
- Shehu Sani
Shehu Sani ya kara da cewa ya kamata ƴan Najeriya su san adadin maƙudan kudin da ƴan majalisa ke karɓa da kuɗin da ake ba su a wata.
Tsohon dan majalisar ya ce a ganinsa babu bukatar a tsaya ana yaudarar ‘yan Najeriya ko kuma a boye wani abu ba.
Majalisa ta umarci a hukunta sarki
Ku na da labarin majalisar dokokin jihar Ogun ta yanke shawarar gurfanar da Olu na Obafemi da ke ƙaramar hukumar Obafemi-Owode, Oba Taofeek Owolabi.
Majalisar ta amince da shawarar gurfanar da sarkin ne bisa zarginsa da hannu dumu-dumu a badaƙalar ƙwacen filaye a yankin masarautarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng