Hadiman Tsohon Gwamna, Ƴan Majalisa da Wasu Ƙusoshi Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Hadiman Tsohon Gwamna, Ƴan Majalisa da Wasu Ƙusoshi Sun Sauya Sheka Zuwa APC

  • Hadiman tsohon gwamnan jihar Ondo da wasu manyan ƙusoshi sun kara rikita PDP ana tunkarar zaben gwamnan
  • Tsohon ɗan majalisar tarayya, tsohon kakakin majalisar dokoki da jiga-jigai sun fice daga PDP zuwa APC a Akure
  • Sun bayyana cewa sun gamsu da salon mulkin shugaban kasa da Gwamnan Ondo shiyasa suka zabi haɗewa da APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo ta gamu da gagarumin koma baya yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamna a wannnan shekarar.

Abokan siyasa da makusantan tsohon gwamnan jihar, Olusegun Mimiko, da manyan jiga-jigai sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

PDP da APC.
Manyan kusosshi da hadiman tsohon gwamna sun sauya sheka daga PDP zuwa APC a Ondo Hoto: PDP Nigeria, Official APC
Asali: Facebook

'Yan adawan da suka koma jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

A cewar The Nation, waɗanda suka sauya shekar sun haɗa da tsohon ɗan majalisar tarayya, Hon Victor Akinjo da tsohon kakakin majalisar dokokin Ondo, Hon Joseph Akinlaja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran manyan ƙusoshin da suka jefar da PDP sun ƙunshi tsohon kwamishinan ayyuka, Hon Jumoke Akindele, Hon Gboluga Ikengboju, Cif Alaba Lad Ojomo da sauransu.

Meyasa suka zaɓi komawa jam'iyyar APC?

Tsofaffin jiga-jigan na PDP sun bayyana cewa sun yanke shawarin komawa APC ne domin cicciɓa jirgin Gwamna Lucky Aiyedatiwa zuwa nasara a zaɓen watan Nuwamba.

A cewarsu, sun dawo APC ne domin haɗa karfi da ƙarfe wajen sauya akalar jihar Ondo zuwa turbar ci gaba da kuma samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Masu sauya shekar sun bayyana hakan ne a wata sanarwar haɗin guiwa da aka rabawa manema labarai a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Sanata daga Arewa ya yi nasara a kotun ɗaukaka ƙara, ya tabbata cikakken ɗan APC

Jiga-jigan sun goyi bayan Tinubu

Sanarwar ta ce:

"Mun amince da cewa ana fuskantar ƙalubale masu tarin yawa a ƙasar nan saboda kura-kuran da aka yi a baya da kuma tasirin ƙoƙarin gyara da shugaban kasa ke yi.
"Amma duk da haka muna ganin manufofin da shugaban ƙasa ya ɗauko za su ceto Najeriya daga halin matsin da ta shiga, wannan ya sa muka ga gara mu dawo a yi da mu."
"A ƴan kwanakin da suka wuce, mun tattara dukkan abokanmu da makusantan mu zuwa APC domin mu ba da gudummuwa a gyara jiharmu da ƙasa baki ɗaya."

APC ta samu ƙaruwa a Ondo

A wani rahoton kuma yayin da ake cigaba da kushe tsarin mulkin APC a Najeriya, jamiyyar tana karbar sababbin tuba wadanda suka baro jam'iyyar PDP

Tsohuwar shugabar matan jam'iyyar PDP da dubban magoya bayanta sun watsar da jam'iyyarsu inda suka shigo APC a jihar Ondo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262