Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar PDP, Ta Faɗi Sahihin Wanda Ya Lashe Zaɓen a 2023

Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar PDP, Ta Faɗi Sahihin Wanda Ya Lashe Zaɓen a 2023

  • Kotu ta sauke ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Igboeze ta Arewa/Udenu daga jihar Enugu, Hon. Simon Atigwe
  • Kotun ta ayyana ɗan takarar Labour Party, Dennis Nnamdi Agbo a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓe a 2023
  • Alkali ya amince da ƙorafin mai shigar da ƙara, ya ce wanda INEC ta ba nasara ba shi ya samu ƙuri'u mafi rinjaye ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Kotun sauraron ƙarafe-ƙorafe zaɓe ta tsige ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Igboeze ta Arewa/Udenu Hon. Simon Atigwe.

Kotun zaɓen ta kuma bayyana ɗan takarar jam'iyyar LP, Dennis Nnamdi Agbo a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen ɗan majalisar Igboeze ta Arewa/Udenu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tsawaita wanda Buhari ya ba mukami a gwamnatinsa

Simon Atigwe da Dennis Nnamdi Agbo.
Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan majalisa ɗaya, kotu ta ce LP ce ta lashe zaɓe a 2023 Hoto: @Enugu_updates
Asali: Twitter

Sakamakon zaben da INEC ta bayyana

Kamar yadda PM News ta rahoto, hukumar zaɓe INEC ta ayyana Hon Atigwe na PDP a matsayin wanda ya samu nasara a cikon zaɓen da aka yi a watan Fabrairu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ta sanar da cewa ɗan takarar PDP ya samu ƙuri'u 23,863, inda ya lallasa babban abokin karawarsa Mista Agbo na LP wanda ya tashi da ƙuri'u 23,226.

Tun farko dai ɗan takarar LP ne ya samu nasara a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, amma kotun ɗaukaka ƙara ta sauke shi, ta ba da umarcin sake zaɓe.

Ɗan takarar LP ya nufi kotu

To sai dai bayan ƙarasa zaɓen a ranar 3 ga watan Fabrairu, INEC ta ba PDP nasara, hakan ya sa Agbo ya garzaya kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

Kara karanta wannan

Atiku ya caccaki Tinubu, ya bayyana inda gwamnatinsa ta samu matsala

Lauyoyinsa sun yi zargin cewa an tafka kuskuren alƙalami a sakamakon da aka tattara kuma ba a bi ƙa'idojin zabe ba da dai sauransu.

PDP v LP: Kotun zaɓe ta yanke hukunci

Da yake yanke hukunci ranar Laraba, 14 ga Agusta, kotun zaɓen karkashin mai shari'a H N Kunaza ta gamsu da ƙarar kuma ta ayyana Dennis Agbo a matsayin sahihin ɗan majalisar Igboeze ta Arewa/Udenu.

Kotun ta ƙara da cewa ba Simon Atigwe ne ya samu mafi rinjayen kuri'u a zaɓen ba, domin mai ƙara na LP ya samu kuri'u 23,221 yayin da PDP ta samu 21,863.

Majalisa ta janye kudirin rera taken Najeriya

A wani rahoton kuma majalisar wakilai ta dakatar da sabon kudurin da aka bijiro da shi domin hukunta wadanda ba sa rera taken Najeriya.

Haka kuma kudurin ya kunshi dokar daurin shekaru ko tara ga masu lalata alamomin kasar nan da wuraren ibada gabanin janye ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262