Jami'iyyar APC Ta Nuna Goyon Baya ga Gwamnan PDP, Ta Fadi Dalilin Hada Kai

Jami'iyyar APC Ta Nuna Goyon Baya ga Gwamnan PDP, Ta Fadi Dalilin Hada Kai

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Rivers ƙarƙashin jagorancin Emeka Beke ta nuna goyon baya ga Siminalayi Fubara
  • Emeka Beke ya bayyana cewa jam'iyyar a shirye take ta yi aiki tare da gwamnan domin ciyar da jihar Rivers gaba
  • Shugaban na APC wanda kotu ta mayar kan muƙaminsa, ya nuna cewa lokacin siyasa ya wuce, ana kan gabar aiki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ƙarƙashin jagorancin Emeka Beke ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara.

Shugaban jam’iyyar APC wanda kotu ta mayar kan kujerarsa, Emeka Beke, ne ya bayyana hakan.

APC ta goyi bayan gwamnan Rivers
Jam'iyyar APC ta nuna goyon baya ga Gwamna Siminalayi Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

APC ta nuna goyon baya ga Gwamna Fubara

Jaridar Tribune ta rahoto cewa Emeka Beke, ya nuna goyon baya ga Gwamna Fubara ne yayin wata hira da wani gidan talabijin a birnin Port Harcourt.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi hanyar da za a iya raba Tinubu da mulkin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na APC ya tabbatar da goyon bayan jam’iyyar ga Gwamna Fubara, inda ya jaddada cewa mutum gwamna ɗaya ne kaɗai zai iya samu a lokaci guda ba biyu ba.

Shin APC za ta yi aiki da gwamna a PDP?

Ya kuma ba da tabbacin cewa idan har gwamnan ya nemi su yi aiki tare, za su mara masa baya domin ganin jihar Rivers ta samu ci gaba, rahoton Tide News ya tabbatar.

"Fubara gwamnan jihar Rivers ne, kuma ba za a iya samun gwamnoni biyu ba. Ko da ɗanka ne ka ba muƙamin gwamna, ya kamata ka bar shi ya yi abin da ya dace."
"Idan ya nemi haɗin kan APC, za mu yi aiki tare da shi domin ciyar da jihar gaba. Ba zai yiwu mu ci gaba da faɗa ba, koma baya jihar Rivers ke samu. Lokacin siyasa ya wuce, yanzu lokaci ne na mulki."

Kara karanta wannan

Atiku ya caccaki Tinubu, ya bayyana inda gwamnatinsa ta samu matsala

- Emeka Beke

Batun biyan N80,000 ga ma'aikata a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Rivers ta musanta rahoton cewa za ta yi wa ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamna Simi Fubara ne ya musanta hakan, inda ya ce gwamnati ba ta ce za ta biya N80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng