Kano: Abba Ya yi Babban Rashi, Ɗan Kwankwasiyya Ya Ajiye Mukami, Ya Koma APC

Kano: Abba Ya yi Babban Rashi, Ɗan Kwankwasiyya Ya Ajiye Mukami, Ya Koma APC

  • Babban jagora a tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano, Abdulrahman Mai Kadaman Kwankwasiyya ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP
  • Haka zalika, Abdulrahman Mai Kadaman Kwankwasiyya ya sanar da yin murabus daga mukamin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba shi
  • Sanata Barau Jibrin ne ya karbi Abdulrahman Mai Kadaman Kwankwasiyya a birnin tarayya Abuja a jiya Talata, 13 ga watan Agusta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Siyasar Kano na cigaba da ɗaukan sabon salo yayin da ake cigaba da samun masu sauya sheka.

Jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Abdulrahman Mai Kadaman Kwankwasiyya ya koma jam'iyyar APC.

Barau Jibrin
Babban dan Kwankwasiyya ya koma APC a Kano. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da fitar Mai Kadaman Kwankwasiyya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Babban jigo ya faɗi dalili 1 da ya kamata a tsige Tinubu da wasu gwamnoni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon Kwankwasiyya ya koma APC

Jigo a tafiyar matasan Kwankwasiyya, Abdulrahman Mai Kadama ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar APC kuma ya zama Mai Kadaman Maliya.

Haka zalika Abdulrahman ya tabbatar da cewa ya ajiye mukaminsa na mai ba Abba Kabir Yusuf shawara.

Mai Kadama ya ajiye jagorancin Kwankwasiyya

Dan siyasar ya bayyana cewa ya ajiye jagorancin tafiyar Kwankwasiyya a Filato da shugabancin G-6 a Kano.

Haka zalika ya bayyana cewa ya ajiye shugabancin kungiyar a kasa a tsare ta Kwankwasiyya a fadin Najeriya.

Kiran jigon Kwankwasiyya ga matasa

Bayan sauya sheƙa, Abdulrahman ya yi kira ga matasa kan shigowa tafiyar APC a jihar Kano domin samun romon dimokuraɗiyya.

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa jam'iyyar APC ita ce kawai za ta kawo sauyi wajen cigaban al'umma a Najeriya.

Yan NNPP sun sauya sheka a Kano

Kara karanta wannan

2027: Tsohon shugaba a APC ya fara yunkurin doke Tinubu, ya tabo Atiku da Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin matasan jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano sun sauya sheka zuwa jami'yyar APC mai adawa a jihar.

Shugabannin matasan sun bayyana sauya shekar ne yayin ganawa da mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin.

Haka zalika matasan sun bayyana dalilai da suka sanya su ficewa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC ga Sanata Barau Jibrin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng