Atiku Ya Caccaki Tinubu, Ya Bayyana Inda Gwamnatinsa Ta Samu Matsala
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya koka kan halin da Najeriya ta tsinci kanta a hannun gwamnatin Bola Tinubu
- Atiku ya bayyana cewa kuskuren da Muhammadu Buhari ya yi wasan yara ne idan aka kwatanta da wanda wannan gwamnatin ke yi
- Atiku ya yi nuni da cewa gwamnatin Tinubu ba ta da wani shiri a ƙasa domin cire ƴan Najeriya daga halin da ta tilasta musu tsintar kansu a ciki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sake caccakar gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.
Atiku ya ce idan har yanzu APC ba ta gane irin wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki ba, hakan na nufin tun farko ba ta shirya yin mulkin ƙasar nan ba.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 ya bayyana hakan ne ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu
Atiku ya bayyana cewa abin takaici ne yadda gwamnati ta jira sai da ƴan Najeriya suka fito kan tituna domin jawo hankalinta wahalar da ake ƙaƙaba musu a ƙasa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
"Tabbas akwai ƙalubale kafin yanzu, shi ya sa aka ba ku mulkin. Mun san abubuwa da yawa an yi kuskure a lokacin Buhari."
"Tattalin arzikin kasar ya durƙushe sau biyu a ƙarƙashin gwamnatin APC da ta shuɗe saboda ba ta san komai ba kan tattalin arzikƙi ga yawan cin hanci da rashawa."
"Duk wani kuskuren da Buhari ya yi yanzu muna ganin wanda ya fi shi a ƙarƙashin Tinubu. Abin da muke gani yanzu wanda ya yiwa na Buhari fintinkau ne.
"Ta yaya farashin kayan abinci zai ragu alhali manoma ba za su iya komawa gonakinsu ba saboda rashin tsaro?
"Abin takaici, babu wani abu a ƙasa da zai nuna cewa wannan gwamnatin ta shirya magance matsalolin al'ummarmu."
- Atiku Abubakar
Atiku ya yi gargaɗi kan matatar Dangote
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi gargadi kan yunkurin da ake yi na ganin bayan matatar man Dangote da gangan.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa matatar man Dangote za ta iya warware matsalar ƙarancin man da ake fama da ita a ƙasar nan da samar da isassun kuɗaɗen ƙasashen waje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng