Zanga Zanga: Babban Jigo Ya Faɗi Dalili 1 da Ya Kamata a Tsige Tinubu da Wasu Gwamnoni

Zanga Zanga: Babban Jigo Ya Faɗi Dalili 1 da Ya Kamata a Tsige Tinubu da Wasu Gwamnoni

  • Tsohon mataimakin shugaban APC na Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya yi iƙirarin cewa tsarin dimokuradiyyar Najeriya ba ya aiki
  • Lukman ya bayyan acewa halin da ƙasar nan ke ciki kaɗai ya isa a sauke shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnoni
  • Fitaccen ɗan siyasar ɗan asalin jihar Kaduna ya nanata cewa ƴan Najeriya sun fusata kuma suna cikin mawuyacin hai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban APC a shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya ce zanga-zangar da aka yi kaɗai ta isa zama dalilin tsige Bola Ahmed Tinubu.

Lukman ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta, 2024, sa'o'i 24 bayan kammala zanga-zangar kwanaki 10 da matasa suka yi.

Kara karanta wannan

Atiku ya caccaki Tinubu, ya bayyana inda gwamnatinsa ta samu matsala

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Salihu Lukman ya yi ikirarin cewa demokuraɗiyyar Najeriya ba ta aiki Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Fitaccen ɗan siyasar ya yi iƙirarin cewa wannan fushi da ƴan Najeriya suka nuna a zanga-zangar ya isa zama dalilin da zai sa a sauke shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Salihu Lukman ya ƙara da cewa zanga-zangar ta kai matsayin da ya kamata a bi hanyar doka wajen sauke gwamnoni da dama daga kan kujerunsu, Vanguard ta rahoto.

Lukman ya caccaki ƴan majalisa

A sanarwar, Lukman ya ce:

"A zahiri tsarin demokuraɗiyyar ƙasar nan ba ya aiki kamar jam'iyyun siyasa da ƴan majalisar dokokin tarayya. Bisa abubuwan da ke faruwa ya kamata a ce Shugaba Tinubu da mafi akasarin gwamnoni sun shiga layin tsigewa.
"Yadda aka maida ƴan majalisar tarayya ƴan amshin shata, ga jam'iyyun siyasa ba su da bakin magana, hakan ne ya tunzura ƴan Najeriya suka fusata har suka zaɓi yin zanga-zanga."

Kara karanta wannan

Gwamna ya feɗewa Tinubu gaskiya, ya faɗa masa halin da ya jefa ƴan Najeriya

Zanga-zangar adawa da gwamnati

Legit Hausa ta kawo muku yadda ƴan Najeriya suka shirya tare da gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan domin nuna fushinsu kan halin ƙuncin da ake ciki.

Bayan shafe kwanaki 10, masu zanga-zangar sun yi barazanar sake shirya wata a watan Oktoba matuƙar ba a samu sauƙi a halin matsin da al'umma ke ciki ba.

Kaduna ta kafa sharadin zanga-zanga

A wani rahoton kuma gwamnatin Kaduna ta gargaɗi matasa cewa ba za ta lamunci duk wata zanga zanga ba tare da izinin hukumomin tsaro ba.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya ce sun gano wasu miyagu da ke shirin fakewa da zanga zanga su tayar da fitina a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262