Ana Rade Radin Gwamnan PDP Zai Sauya Jam'iyya, Tsageru Sun Jefa 'Bam' Ofishin APP

Ana Rade Radin Gwamnan PDP Zai Sauya Jam'iyya, Tsageru Sun Jefa 'Bam' Ofishin APP

  • Yayin da barakar da ke tsakanin Siminalayi Fubara da Nyesom Wike ke kara kamari, an fara yada labarin gwamnan zai koma APP
  • Sai dai an wayi gari da tarwatsewar sakatariya jam'iyyar APP bayan wasu tsageru sun jefa abin fashewa da misalin 1: 00 na safiya
  • Duk da ba a samu asarar rayuka ba, amma an lalata dukiyoyi da ginin ofishin, wanda 'yan jam'iyyar ke ganin harin ya jibanci siyasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers - Wani abin fashewa da ake kyautata zaton bam ne ya tarwatsa sakatariyar jam'iyyar APP da ke yankin Fatakwal a jihar Ribas da tsakar dare, wayewar Litinin.

Kara karanta wannan

An samu sabanin tsakanin 'yan sanda da rundunar sojoji a kan harbin 'yan zanga zanga

Wasu tsageru ne su ka bi dare tare da jefa abin fashewar, wanda nan take ya tarwatsa tagogi da saman kwanon ofishin da sauran kayan da ke ciki.

Sir Siminalayi Fubara
Ana zargin gwamna Fubara zai koma APP, tsageru sun tarwatsa ofishin jam'iyyar Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa wasu daga cikin 'yan jam'iyyar na ganin an kai hari ofishin ne saboda manufa ta siyasa, ganin yadda APP ke kara tumbatsa a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin gwamna Fubara zai koma APP

Ana jita-jitar gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara zai fice daga jam'iyyarsa ta PDP zuwa APP bisa zargin yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike ya hana shi sakat.

Ana tsaka da batun sauya shekar ne aka kai hari sakatariyar APP a ranar Litinin, kamar yadda Jaridar Vanguard ta wallafa.

Wani dan jam'iyyar APP mai suna Chimene ya bayyana cewa su na zargin an kai masu hari ne saboda karuwar farin jininsu a Ribas, inda ya bukaci jami'an tsaro su gaggauta bincike.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Majalisar matasan Arewa ta yi fatali da neman dauke cibiyar NCC daga Kano

Gwamnonin PDP sun goyi bayan Fubara

A baya mun ruwaito cewa gwamnonin jam'iyyar PDP sun zabi bangare a rikicin da ke ci gaba da ruruwa tsakanin gwamna Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Gwamnonin ta cikin wata sanarwa da su ka fitar sun nuna goyon bayansu ga gwamna Siminalayi Fubara, tare da neman masu ruwa da tsaki su taimaka wajen shawo kan rikicin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.