An Yaba Jawabin Tinubu, an Nemi Ya Cafke Dan Takarar Shugaban Kasa Kan Tutar Rasha

An Yaba Jawabin Tinubu, an Nemi Ya Cafke Dan Takarar Shugaban Kasa Kan Tutar Rasha

  • Wata kungiyar Yarbawa a Najeriya ta yi magana kan jawabin Shugaba Bola Tinubu a karshen makon da ya gabata
  • Kungiyar ta ce abin yabawa ne yadda Tinubu ya warware matsalolin da ke cikin korafin masu zanga-zanga a jawabinsa
  • Shugaban kungiyar, Hassan Oladotun ya bukaci Tinubu ya kama dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Omoyele Sowore

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Yarbawa ta yabawa Shugaba Bola Tinubu kan jawabin da ya gabatar.

Kungiyar ta ce Tinubu ya magance matsalolin da yan kasar ke fuskanta yayin gabatar da jawabin nasa.

Kungiya ta yabawa jawabin Tinubu, ta ba shi shawara
Kungiya ta yabawa jawabin Bola Tinubu inda ta ce ya wanke masu zanga-zanga. Hoto: Hassan Oladotun, Nurphotos.
Asali: UGC

Zanga-zanga: An yabawa jawabin Bola Tinubu

Shugaban kungiyar, Hassan Oladotun shi ya bayyana haka ga jaridar Legit a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon PDP ya fadi yadda Tinubu zai magance matsalolin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oladotun ya ce jawabin Tinubu ya tabo duka matsalolin masu zanga-zanga da ma sauran korafe-korafe.

"Maganar gaskiya duk wanda ya kushe jawabin Tinubu to yana da karamin tunani ne kawai."
"Tinubu ya yi magana kan duka matsalolin da ke damun masu zanga-zanga da kuma baje su domin kawo mafita."

- Hassan Oladotun

Tutar Rasha: An bukaci kama dan takara

Har ila yau, Kungiyar ta bukaci cafke dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore kan daga tutocin Rasha yayin zanga-zanga.

Ta ce daga tutar Rasha cin amanar kasa ne kuma goyon bayan da Sowore ya yi ya kamata a kamashi saboda cin dunduniyar Najeriya.

Ana zargin Sowore da goyon bayan zanga-zangar da ma daga tutocin Rasha da wasu suka riƙa yi musamman a Arewacin Najeriya.

Kungiya ta gargadi gwamnan PDP kan Tinubu

Kun ji cewa wata kungiya a Arewacin Najeriya ta gargadi Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi kan kalamansa.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fadawa Tinubu hanyar da zai shirya da talakawa bayan zanga zanga

Kungiyar Arewa Young Leaders Forum (AYLF) ta yi gargadin ne bayan gwamnan ya yi shagube ga Bola Tinubu kan zaben 2027.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa ta musamman da kungiyar ta fitar a yau Juma'a 9 ga watan Agustan 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.