"Ba Haka Ba ne," Gwamna Ya Maida Martani kan Ikirarin Tinubu na Rabawa Jihohi N570bn
- Gwamna Seyi Makinde ya musanta ikirarin Bola Ahmed Tinubu na rabawa jihohi N570bn domin ragewa al'umma raɗaɗin kuncin rayuwa
- Tun farko shugaban ƙasa ya ce gwamnatinsa ta rabawa gwamnoni maƙudan kuɗi domin su faɗaɗa shirye-shiryen tallafawa ƴan Najeriya
- Da yake mayar da martani bayan wani ɗan jihar Oyo ya nemi ƙarin haske, Makinde ya ce kudin da ake magana na tallafin COVID-19 ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya musanta ikirarin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na rabawa jihohi 36 tallafin rage raɗaɗi har N570bn.
Da yake jawabi kan zanga-zangar da aka fara, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta rabawa gwamnoni N570bn domin rage raɗaɗin halin da ake ciki.
“An tura N570bn zuwa jihohi 36 domin fadada tallafin ragewa ƴan Najeriya raɗaɗi, yayin da ‘yan kasuwa 600,000 suka ci gajiyar tallafin ƙanana da matsakaitan sana'o'i,"
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Bola Tinubu.
Gwamna Makinde ya musanta ikirarin Tinubu
Amma a wata sanarwa da Gwamna Makinde ya rattaɓawa hannu da kansa kuma ya wallafa a shafinsa na X, ya ce jihar Oyo ba ta da labarin wannan tallafin.
Gwamna Makinde ya ce kuɗin da ake ta kai komo a kansu N570bn ba tallafi ba ne daga gwamnatin tarayya, sun fito ne daga Bankin Duniya.
Ya bayyana cewa kudaden sun ta’allaka ne kan abin da jihohin suka rigaya suka kashe kan shirye-shiryen COVID-19.
Seyi Makinde ya ce Bankin Duniya ya maidawa jihohin kuɗin da suka yi amfani da su wajen magance tasirin cutar.
Wane kuɗi gwamnoni suka karɓa?
“A cikin jarida ta daren yau, na amsa tambaya daga wani dan jihar Oyo game da ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta ba jihohi sama da N570bn a matsayin wani ƙunshin kuɗin tallafawa talakawa."
"Bari na fayyace muku gaskiya dalla-dalla, kuɗin da ake ta ɓaɓatu a kansu wani ɓangare ne na tallafin da Bankin ke bai wa tsarin NG-CARES, wanda ake tallafawa al'umma."
- Gwamna Seyi Makinde.
Wannan kalamai na Makinde na zuwa a daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula da ɓarnar dukiya sakamakon zanga-zangar da aka fara a farkon watan Agusta.
Za a kafa kamfanin siminti a Bauchi
A wani rahoton kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fara aikin gina masana'antar siminti.
Mohammed ya rattaɓa hannu kan yarjejeniyar MoU da kamfanin Resident Cement Factory Limited na fara gina masana'antar a farkon 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng