An Samu Baraka Tsakanin Shugaban Majalisar Tarayya da Mataimakinsa? An Gano Gaskiya

An Samu Baraka Tsakanin Shugaban Majalisar Tarayya da Mataimakinsa? An Gano Gaskiya

  • Majalisar Wakilai ta kore jita-jitar da ake yadawa na baraka tsakanin Shugabanta, Hon. Tajudden Abbas da mataimakinsa
  • Majalisar ta ce akwai alaka mai kyau tsakanin Abbas da mataimakinsa, Hon. Benjamin Kalu sabanin yadda ake yadawa
  • Wannan na zuwa ne bayan Majalisar ta rusa kwamitin kula da albarkatun mai wanda ake tunanin sun samu baraka tsakaninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai a Najeriya ta yi martani kan jita-jitar cewa akwai matsalar jituwa tsakanin shugabanninta.

Martanin na zuwa ne bayan yada cewa alaka ta yi tsami tsakanin shugaban Majalisar, Hon. Tajudden Abbas da mataimkinsa, Benjamin Kalu.

Majalisa ta yi karin haske kan baraka tsakanin shugabanninta
Majalisa ta karyata jita-jitar rigima tsakanin shugabanta da mataimakinsa. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Majalisa ta magantu kan baraka tsakanin shugabanninta

Kara karanta wannan

Ana ƙoƙarin shawo kan Ndume, dan majalisa ya kara tsige gaskiya ga Tinubu

Mai magana da yawun Majalisar, Akin Rotimi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan bai rasa nasaba da rusa kwamitin kula da albarkatun mai da aka yi a Majalisar bisa kundin tsarin mulkin 1999.

Rotimi ya ce Majalisar ta dauki matakin ne domin tabbatar da gudanar da aiki yadda ya kamata da kuma kaddamar da bincike.

"Shugabannin Majalisar suna da damar rusa duk wani kwamiti da suka ga ya cancanta a dauki mataki a lokacin da ya dace."
"Wannan mataki na Majalisar na rusa kwamitin domin gudanar da bincike kan matsalolin da ke tattare da shi bai saba ka'ida ba."
"Babu wata matsala tsakanin shugaban Majalisar da mataimakinsa kan wannan lamari kuma suna da kyakkyawar alaka a tsakaninsu."

- Akin Rotimi

Majalisa ta bukaci al'umma su guji jita-jita

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Majalisar matasan Arewa ta yi fatali da neman dauke cibiyar NCC daga Kano

Rotimi ya ce akwai alaka mai kyau tsakanin shugabannin Majalisar inda ya ce ba za su bar wani abu ya lalata tsakaninsu ba.

Ya bukaci al'umma da su guji yada wannan jita-jita musamman a kafofin sadarwa saboda babu kamshin gaskiya a cikinta.

Halin kunci: Dan Majalisa ya shawarci Tinubu

Kun ji cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Idemili ta Kudu da Arewa ya tura sako ga Bola Ahmed Tinubu kan tsadar rayuwa.

Dan majalisar ya fadi abin da ya kamata shugaban kasa Tinubu ya yi a kan halin da al'umma ke ciki a Najeriya musamman na tsadar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.